Batun karantun Alkur’ani a lokacin bikin bude Gasar Cin Kofin Duniya da ke gudana a kasar Qatar ya dauki hankalin al’ummar duniya.
Duk da cewa a lokacin bikin bude gasar ta bana, Jakadan Kofin Duniya na FIFA, Ghanim Al Muftah, ya karanta wata aya daga cikin Alkur’ani, masu amfani da kafofin sada zumunta sun yi ta yada wani bidiyo tare da ikirarin cewa na bikin ne.
Miliyoyin masu amfani da kafofin sada zumunta a fadin duniya ne suka kalli wani bidiyo da ke nuna wasu kananan yara na karatun Alkur’ani a gaban malami a tsakiyar wani filin wasa.
Masu yada bidiyon da ya yi tashe sun yi ikirarin cewa na bikin bude Gasar Kofin Duniya a ta 2022 Qatar ne a Filin Wasa na Al Bayt da ke Doha, babban birnin kasar.
Wani wanda ya wallafa bidiyon a Facebook da harshen Urdu ya rubuta cewa, “Qatar ce kasar Musulunci da ta fara karbar bakuncin Gasar Cin Kofin Duniya na FIFA da aka bude gasar da gabatar da karatun Alkur’ani. #FIFAWorldCup #FIFAWorldCupQatar2022.”
Akalla mutum miliyan uku ne suka kalli bidiyon da ya wallafa; akwai kuma wadanda suka sa irin bidiyon a Twitter, TikTok da Facebook da aka kalla sama da sau dubu 500.
Wannan bidiyo ya yi tashe ne tun a yayin da ake shirin fara wasannin gasar a ranar Lahadi 20 ga watan Nuwamba, 2022 a Filin Wasa na Al Bayt.
Tsohon bidiyo ne
Sai dai kuma binciken da Kamfanin Dillancin Labaran Faransa na AFP ya gano cewa bidiyon karatun Alkur’ani da yaran suka yi an dauke shi tun a watan Oktoban shekarar 2021.
Binciken ya kuma gano cewa shi wannan tsohon bidiyon na bikin bude Filin Wasa na Al Thumama ne, ba na bikin bude Gasar Kofin Duniya na Qatar 2022 ba.
Binciken da aka gudanar a YouTube ya gano cewa tun ranar 13 ga watan Oktoba, 2021 kafar yada labarai ta Alrayyan TV da ke Qatar ta wallafa bidiyon, wanda yanzu ake yadawa — akalla shekara daya da wata daya kafin Gasar Kofin Duniya na Qatar 2022.
A tare da bidiyon da Al rayyan TV ta wallafa, an rubuta da Larabci cewa, “Wannan shi ne bikin bude Filin Wasa na Al Thumama, inda za a buga Gasar Kofin Duniya a Qatar a 2022.”
A cikin bidiyon na asali da Al Rayyan ta saka a YouTube, an fara karatun ne a daidai minti 2:45, inda kuma za a ga tambarin tashar a rubuce da Larabci.
Za kuma a iya samun wannan bidiyo da kafar Al Jazeera ta kasar Qatar ta wallafa na bikin bude Filin Wasa na Al Thumama a 2021.
Hukumar Kwallon Kafa ta Duniya (FIFA) ta bayyana ta ce a ranar 22 ga watan Oktoba, 2021 ne aka yi bikin bude Filin Wasa na Al Thumama da ke birnin Doha a hukumance, gabanin Gasar Kofin Duniya.
A ranar ce kuma aka buga wasan karshe na Gasar Cin Kofin Amir na kasar a filin wasan, shekara guda kafin ya karbi bakuncin Gasar Kofin Duniya.
Kasar Qatar ta kashe kimanin Dala biliyan 226 wajen karbar bakuncin gasar, wanda shi ne mafi tsada a tarihinta.
Kawo yanzu, an sayar da tikitin kallon wasanni kimanin miliyan uku, duk da cewa mutum miliyan 1.3 ne aka fara hasashen za su je kallon.
Hukumar FIFA ta ce zuwa ranar Litinin, kwana guda da fara gasar, kudaden shiga da ta samu ya zarce Dala biliyan 7.5, kuma ya wuce abin da ta yi hasashen samu.
Gasa mai cike da rudani
Ce-ce-ku-ce ya dabaibaye yadda Qatar ta samu zama mai masaukin bakin tun shekara 2010.
An yi zargin rashawa wajen ba wa Qatar daukar nauyin gasar, zargin da ta sha karyatawa, kuma an wanke ta daga gare shi.
Duk da haka, dambarwar ta yi sanadiyar haramta wa wasu manyan jami’an FIFA shiga harkar kwallon kafa har abada.
A hannu guda kuma, kungiyoyin kare hakki sun yi ca a kan kasar kan zargin tauye hakkokin ma’aikata ’yan kashen waje da kuma takura wa ’yan luwadi da madigo.
Sannan akwai dokokin Musulunci da kasar take dabbakawa, kamar haramta shan giya da bayyana tsiraici da kuma cudanya tsakanin maza da mata da sauransu.
Wadannan sun sa an yi hasashen gasar ba za ta yi armashi ba, amma kuma duk da haka sai ga shi masu zuwa kallo sun kusa ninka adadin da aka yi hasashe.
Aminiya ta kawo rahoton yadda ’yan kallo ke shafe tsawon lokaci suna jiran samun tikitin kallon wasannin gasar.
Gasar dai ita ce ta farko da wata kasar Musulunci ko a yankin Gabas ta Tsakiya ta zama mai masaukin baki.