✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bill Gates zai yi bincike kan mutuwar yara

Hamshakin mai arzikin nan wanda ke da kamfanin Microsoft, Bill Gates, ya bayyana shirinsa na kafa cibiyoyin kiwon lafiya a nahiyar Afirka da kuma Asiya…

Hamshakin mai arzikin nan wanda ke da kamfanin Microsoft, Bill Gates, ya bayyana shirinsa na kafa cibiyoyin kiwon lafiya a nahiyar Afirka da kuma Asiya domin rage mutuwar kananan yara da yin rigakafin cututtuka irin su Ebola.

Mista Gates ya shaida wa BBC cewa zai kafa cibiyoyin lafiya guda shida wadanda za su yi saurin gano cututtukan da za su iya barkewa ta yadda za a shawo kan su cikin gaggawa.
Mista Gates, wanda ya kafa gidauniyar The Gates Foundation da ke taimaka wa al’umma, ya ce zai ware Dala miliyan 75 a matsayin kafin-alkalami domin kafa cibiyoyin kiwon lafiyar.
Ya rubuta a shafinsa na Intanet cewa duniya ta samu ci gaba sosai ta fuskar mutuwar yara a cikin shekara 25.
“A shekarar 1990, yaro daya ne yake mutuwa cikin kowane yara 10. Amma saboda rigakafi da abinci mai inganci sun sanya a yau yaro daya yake mutuwa cikin yara 20,” inji shi.
Attajirin yana daga cikin manyan masu kudi a duniya wadanda ke bayar da gagarumar gudunmawa wajen ci gaban kasashe.