✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Bill Gates zai kai wa Afghanistan dauki don yakar cutar shan-inna

Tuni abokan huldar gidauniyar Bill & Melinda Gates suka gana da Taliban a Qatar

Hamshakin attajirin duniya kuma mamallakin kamfanin Microsoft, Bill Gates, ya ce a shirye yake ya gana da gwamnatin Taliban muddin hakan zai taimaka wajen kawar da cutar shan-inna a kasar Afghanistan.

Bill Gates ya fada wa jaridar Telegraph a ranar Litinin cewa, zai yi bakin kokarinsa wajen tallafa wa yaki da shan-inna a kasar ta hannun Gidauniyarsu ta ‘Bill and Melinda Gates’.

Ya ce tuni abokan huldar gidauniyarsu suka gana da Taliban a Qatar, tare da nuna jin dadinsa kan yadda kasar ta kyale ministan lafiyarta saboda a cewarsa, yana da sanin makamar aiki.

Gates ya nuna damuwarsa kan yadda shugabannin duniya ba su ba da muhimmanci yadda ya kamata ba wajen yaki da wannan cuta ta shan-inna.

Cutar shan-inna, cuta ce mai hadarin gaske wadda ka iya shanye sassan jiki cikin kankanin lokaci idan an kamu da ita, musamman ma a tsakanin kananan yara.

A halin da ake ciki, cutar na ci gaba da addabar kasashen Afghanistan da Pakistan, kamar yadda Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta bayyana.