Attajirin nan na Amurka wanda ke fadi-tashin ganin an samar da rigakafin COVID-19, Bill Gates, ya kamu da cutar.
Ya tabbatar da hakan ne a shafinsa na Twitter ranar Laraba.
- Lyon ta dakatar da dan wasanta saboda tsananin banka tusa
- Dan majalisa na son China ta ceto fasinjojin jirgin kasan Kaduna
Ya ce, “Na fara fuskantar kananan alamomin cutar COVID-19, amma ina bin shawarwarin likitoci kuma na killace kaina har sai na ji dama-dama.”
Sai dai ya ce ya yi sa’a cewa an yi masa rigakafin cutar tun gabanin kamuwar shi da ita.
Attajirin, wanda shi ne mamallakin kamfanin Microsoft, a karon farko ya yi taro da ma’aikatansa ta intanet cikin shekara biyu, kamar yadda gidan talabijin na CNN ya rawaito.
A wata hirarsa da gidan talabijin din a bara, Bill Gates ya ce yana fatan ganin an kawo karshen cutar nan da 2023.
Gidauniyar attajirin mai suna Gates Foundation ta kashe sama da Dalar Amurka biliyan 1.75 wajen yaki da cutar a fadin duniya.