✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Biliyan N250 Matawalle ya wawushe a Zamfara —Gwamna Lawal

Dauda Lawal ya ce fanko Bello Matawalle ya bar a asusun jihar kuma N70bn da EFCC ta fara ganowa ya karkatar wasan yara ne

Gwamnan Zamfara, Dauda Lawal ya ce tsohon gwamna Bello Matawalle ko taro bai bari a asusun jihar ba, lokacin ya sauka daga mulki.

Dauda Lawal ya bayyana hakan ne a shirin Politics Today na gidan talabijin na Channels.

Ya ƙara da cewa bayan da ya karɓi mulki, ya gano cewa an yi sama da faɗi da kusan Naira biliyan 250.

Gwamna Dauda Lawal ya ce, “EFCC ta yi iƙirarin a ranar 21 ga Mayu, 2023 cewa tana zargin an sace Naira biliyan 70. Ma’ana kafin in hau mulki.

“A lokacin da na karɓi mulki, na gane cewa Naira biliyan 70 da suka ambata wasan yara ne.

“A yanzu haka bisa bayanan da na samu, mun gano cewa an yi sama da faɗi da Naira biliyan 250.

“Bari in bayyana muku halin da jihar da na gada ke ciki: Jihar ba ta aiki lokacin da na hau kan mulki.

“Lokacin da na karɓi mulki babu Naira miliyan 4 a asusun gwamnatin jihar Zamfara – fanko kawai.

“Ma’aikata na bin jihar bashin albashin watanni hudu.

“A cikin shekaru uku babu wani ɗan jihar Zamfara da ya rubuta WAEC ko NECO, dai da na ware Naira biliyan 1.3 na NECO da Naira biliyan 1.6 na WAEC.

“Wasu daga cikin ɗaliban sun karbi satifiket dinsu ne bayan kammala biyan kudin WAEC da NECO da na yi,” in ji Dauda Lawal.

Gwamnan ya ƙara da cewa bai taɓa baiwa ’yan bindiga ko kwabo ba, yana mai cewa ba zai taɓa yin sulhu da su ba.