Gwamnatin Jihar Zamfara, ta amince da Naira 70,000 a matsayin sabon mafi ƙarancin albashi ga ma’aikatan jihar.
A wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ya bayyana cewa daga yanzu za a fara biyan sabon albashin ga ma’aikatan jihar.
- Sojoji sun lalata haramtattun matatun mai 20, sun ƙwato litar mai 90,000
- ’Yan sanda sun ceto mutum 3 daga hannun ’yan bindiga a Nasarawa
Sanarwar ta kuma ce gwamna Dauda Lawal, ya amince da ƙarin albashi na wata ɗaya ga ma’aikata don taimaka musu yayin bukukuwan ƙarshen shekara.
“Wannan shi ne karon farko a tarihin Jihar Zamfara da aka samu irin wannan ci gaban, kuma an fara biyan ƙarin ne tun a watan Disamba,” in ji sanarwar.
Hakazalika, dukkan ma’aikata, ciki har da waɗanda suka yi ritaya, za su samu ƙarin kashi 30 cikin 100 na alawus ɗinsu.
Gwamna Dauda, ya bayyana cewa wannan sabon albashi da alawus ɗin na nufin tallafa wa ma’aikata da ƙara musu ƙarfin gwiwa domin su ci gaba da aiki tuƙuru wajen bunƙasa jihar.