Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Yobe, Yahaya S. Abubakar, ya lashi takobin yaki da ’yan ta’adda da kuma kare rayukan al’umma a lokacin bukukuwa da ma bayan Babbar Sallah.
Ya ba da tabbacin ne a jawabinsa ga kwamandojin shiyya da manyan jami’an ’yan sandan masu kula da bangarori daban-daban, inda ya hore su da su samar da dukkannin matakan tsaro a lokacin bukukuwan sallah.
- Ku sa ido sosai kan baki masu shigowa – Sarkin Fika
- An yi yunkurin caka wa Shugaban Mali wuka a filin Idi
Wannan batu yana kunshe ne a sankon da kakakin ’yan sandan jihar ta Yobe, ASP Dungus Abdulkarim ya sanya wa hannu.
Rundunar ta bukaci al’ummar Jihar Yobe da su zama masu da’a da biyayya ga dokar kasa da na hanya, su guje wa tukin ganganci wanda a cewarsa hakan zai taimaka wajen kara samar da zaman lafiya a jihar.
Sannan ya gargadi jami’an tsaro da su zama masu nuna kwarewa a yayin gudanar da ayyukansu tare da kare hakkin ’yan kasa.
Daga nan sai kwamishinan ’yan sandan ya taya al’ummar Musulmi murnar zagayowar Babbar Sallah, ya kuma hori al’umma da su zama masu sanya ido kan duk wani abu da ba su aminta da shi ba.