Akalla jami’an tsaron 5,350 ne za a girke don tabbatar aminci a yayin bukukuwan Sallah Karama a Jihar Kwara.
Hadin gwiwar jami’an ’yan sandan da jami’an tsaron NSCDC, za a girke za su ne domin sanya ido kan manyan ababen hawa da kuma zirga-zirgar mutane a jihar.
- Mutum 15 sun rasu a hatsarin kwalekwale
- ’Yan bindiga sun sa cikina ya zube —Dalibar Afaka
- Gobara ta cinye kantuna 91 a kasuwar tufafi
- Mai shekara 25 ta haifi ’ya’ya tara
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, Ajayi Okasanmi ne ya sanar da hakan ga manema labarai, yayin tattaunawarsa da su a ranar Litinin.
Okasanmi, yayin da yake taya al’ummar Musulmi murnar Sallah Karama a jihar, ya ce hukuma ba za ta lamunci aikata laifuka daga bata-gari ba a yayin bukukuwan sallah.
Kazalika, Kwamandan Hukumar Kiyaye Hadura (FRSC) reshen jihar, Jonathan Owoade ya shaida wa manema labarai cewa, hukumar ta su za ta girke jami’anta 1,500 da mototcin sintiri 40 don tabbatar da bin dokokin tuki a jihar.
Har wa yau, gamayyar kungiyar ’yan banga a jihar, za su girke dakarunsu har 1,500 a sassam jihar.