A ranar Asabar za a mika wa Mai Martaba Sakin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero sandar sarauta. Sarkin, wanda shi ne Sarki na 15 a Gidan Sarautar Fulani, ya bayyana wa Aminiya tarihinsa da tasowarsa da kuma alakarsa da sauran masarautun Jihar da aka kiriKiro daga tsohuwar Masarautar Kano. Har wa yau Sarkin ya bayyana hanyoyin da za a bi wajen shawo kan matsaloli da kalubalen da kasar nan take fuskanta:
Yaya za ka bayyana tasowarka a wannan fada har zuwa kasancewarka Sarki a cikinta?
Ina godiya ga Allah da wannan baiwa da Ya yi min domin abin alfaharin kowane da ne ya gaji magabatansa; iyaye da kakanni. Babu shakka mun taso a fada ne ga shi yanzu mun zamo manya a fadar. Da farko dai batutuwa ne guda biyu hakan ya kunsa.
- Yadda El-Rufa’i ya cire dansa daga makarantar gwamnati a cikin sirri
- Tufka Da Warwara: Labari na biyu a gasar Aminiya-Trust
Na farko girmana a matsayin da, inda na koyi darussa da dama a addinance da al’adance a wannan fada.
Abu mafi muhimmanci shi ne irin yadda muka taso ba tare da sanin bambanci a tsakanin wane da wane ko wani da ba jinin sarauta ba! Dukkanmu daya muke daukar kanmu ba tare da wariya ko nuna bambanci ba. Mun taso ne a matsayin ’yan uwa maza da mata tare da ’yan uwantaka da duk wani dan Najeriya ba lallai sai dan Jihar Kano ba.
Duk lokacin da mutane suke tambayata kan yaya tasowata ta kasance, nakan fada musu cewa ba ta da bambanci da tasowar kowane yaro.
Duk da cewa yanayin inda ka tsinci kanka kan taka nasa rawar, amma dai mafi muhimmanci shi ne al’adar iri daya ce, ke nan abin da muka koya a nan na mutunci, shi ne abin da sauran ’ya’ya suka koya daga wajen iyayensu, bambancin kawai wajen yanayin koyarwar ce a tsakanin wannan da wancan wanda hakan na iya faruwa da kowa ma.
Mun gode wa Allah da irin tarbiyyar da aka ba mu sannan mun gode wa iyayenmu da irin shiriyar da suka dora mu a kai sannan mun gode wa al’umma da irin taimaka mana da suka yi har muka kai inda muke a yanzu.
Wacce gudunmawa hakan ta yi a rayuwarka ta yadda ka iya tattaro mutane daban-daban a Jihar Kano da wajenta?
Lamarin yadda na fada ne a baya tun muna yara mun taso ne ba tare da sanin wani bambanci a tsakanimu ba, kuma hakan ya taimaka mana sosai.
Mun taso ne a hade kuma muna yin komai a tare tun daga firamare ta gwamnati inda muke gwamutse da kowa da kowa.
Na yi makarantar firamare ta nan Kofar Kudu daga nan na sake wuce sakandaren gwamnati har zuwa jami’a inda na hadu da mutane daban-daban daga kowanne sashi kuma na yi mu’amala da su.
Babu shakka hakan ya taimaka min sosai a rayuwata, sai dai duk da haka, irin gudunmawar da iyayenmu suka bayar ita ce mafi muhimmanci da kuma tasiri inda suka nuna mana hanyar rayuwa mai kyau da muke girmama na gaba da mu, sannan muke kaunar na kasa da mu tare da zaman lafiya da kowa.
Ana shirin bikin ba sandar sarautar a ranar Asabar, Yaya kake ji a ranka kuma yaya kake kallon lamarin?
Alhamdulillah. Gaskiya idan na ce ba na jin dadi ma ba za ku yarda da ni ba. Amma yanayi mafi farin ciki a rayuwata shi ne lokacin da aka ce ni ne na zama Sarkin Kano, lura da cewa na hau gwadaben iyaye da kakannina.
Da ma sandar sarauta tana tare da mu tuntuni yanzu bikin bayar da sandar sarauta ce kawai wadda Turawan mulkin mallaka suka zo da shi daga baya ya zamo al’ada, shi ne kawai ya rage don kammalawa.
Gaskiya ina matukar jin dadi da jama’ar Kano da Najeriya baki daya musamman farin cikina akan adda na kai matakin da duk wani dan sarauta ke burin kaiwa.
Komai lokaci ne, ina godiya ga Allah da irin baiwar da Ya yi min ta zamowa Sarki ba don na fi kowa iyawa ko arziki ko girma ko wayo ba, sai dai kaddarar Allah kawai a kaina. Kuma ina fata da kuma rokon Allah wajen ba ni damar bayar da gudunmawata wajen ci gaban al’ummata da kuma Jihar Kano baki daya.
Lura da halin da jihar ke fuskanta musamman ta bangaren matasa, ta ina kake ganin masarautun gargajiya za su iya bayar da gudunmawa wajen tunkarar kalubalen ta hanyar mara wa shugabannin siyasa baya wajen rage matsalolin da ake ciki?
A hakika masarautu an samar da su ne don taimaka wa al’umma ba wai ’yan siyasa kadai ba, domin al’umma ita ce wajen dubawa na farko. Za mu fara duba yadda za mu inganta rayuwar matasa.
Muna maganar al’umma ce a dunkule ba wai ’yan siyasa kawai ba. Don haka idan ana maganar ta ina sarakuna za su shigo don bayar da gudunmawa shi ne ta fuskar siyasa, da shugabannin gwamnati sannan ga malaman addini har a gangaro zuwa kan matasa sannan ita kanta masarautar har zuwa kan harkokin tattalin arzikin jama’a.
Ina ganin wajibinmu ne duba yadda za mu taimaka musamman wajen dawowa da habaka tarbiyyar al’ummarmu.
Wannan kalubalen gama-gari ne da ake fama da shi a kasashe ba kawai Jihar Kano ba. Amma a matsayinmu na masu kula da al’adu za mu yi iya kokarinmu don tabbatar da ganin mun mikar da matasa daga inda suka karkace tare da ilimantar da su da kuma bayar da shawara ga wadanda suke cikin gwamnati ta hanyoyin da muka ga iyayenmu suna bi don dorawa daga inda suka tsaya.
Matukar mun kyautata niyyarmu, to, Allah zai taimake mu wajen magance matsalolin da suka addabe mu.
Wadansu suna kiran a kara wa sarakuna karfi domin bayar da muhimmiyar gudunmawa da fiye da yadda suke da shi. Ko kai ma kana goyon bayan haka?
Ni dai tun farko na riga na fada kuma zan ci gaba da fada cewa sarakuna da malaman addini na da gudunmawar da suke bayarwa ko suna cikin kundin tsarin mulki ko ba su a ciki. Amma tunda zamani ya canja kuma jama’a da dama a ganin kundin tsarin mulki shi ne sha-kundum wajen shugabancin al’umma, ba zan ce masu kiran a ba mu aiki cikin kundin tsarin mulki sun yi kuskure ba.
Ni dai na san malamai da sarakuna na da gagarumar gudunmawar da suke bayarwa.
Yaya alakarka take da sauran masarautun Jihar Kano musamman yanzu da ake da masarautun Karaye da Rano da Bichi da kuma Gaya. A matsayinka na Shugabantar Majalisar Sarakunan jihar, ta yaya za ka janyo su duka wajen ganin sun hidimta wa jihar baki daya?
Haka ne. Wadansu na kallon lamarin kamar wani bako, amma mun saba da hakan. Kafin a kirikiro Jihar Jigawa muna da Masarautar Kano da ta Hadeja da ta Gumel da kuma ta Kazaure kuma dukkansu sarakuna ne masu daraja ta daya, kuma ko a lokacin Sarkin Kano shi yake jagorantarsu a matsayin Shugaban Majalisar Sarakuna a lokacin.
Don haka ba wani sabon abu ba ne yanzu da Kano ta samu masarautu biyar bayan kasancewarta a baya da Sarki daya. Don haka duk lokacin da wani abu makamancin haka ya zo, nakan koma in waiwayi tarihi ne don koyon yadda magabatana suka yi suka gama lafiya.
Ba na kallon wata matsala a matsayina na mai shugabantar Majalisar Sarakunan Jihar Kano da sauran masarautun. Abin da ya zame mana bako kawai shi ne yadda ba a dade a sarautar Kano ba, cikin kankanen lokaci aka kacalcala ta zuwa masarautu.
Kada ka manta a lokacin ni aka ba sarautar Bichi kuma na yi iya kokari na don sasanta dan karamin sabanin da ke akwai. Don haka akwai kyakkawar alaka a tsakaninmu kuma muna aiki tare don yi wa al’umma aiki.
Kafin nada ka Sarkin Bichi ka rike sarautar Wamban Kano da wasu sarautu daban-daban ta yadda mutane ke kallonka a matsayin wanda ke da kwarewa. Yaya dangantakarka take da masu rike da irin sarautun da ka rike a baya a halin yanzu?
Mai martaba Sakin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero Haka dai lamarin yake, yana ta maimaita kansa. Sama da shekara 30 ina cikin tsarin tun 1990 kuma na yi wa lamarin kyakkyawar fahimta. Na san wadanda suke sama da ni da wadanda suke kasa da ni kamar yadda na san wadanda muke daidai da su a masarauta. A tsawon shekara 30 da na yi a cikin sarauta, ina girmama duk wadanda suke sama da ni kuma sun rike ni hannu bibbiyu sun jawo ni a jika wanda hakan ya sa na koyi abubuwa da dama daga wajensu.
Ina kallonsu ne a matsayin iyayena kuma na samu kwarewa a wajensu da dama kuma har yanzu da wannan kwarewar nake yin aiki. Su kuma wadanda suke kasa da ni, su ma sun ba ni girmana kamar yadda ni ma na girmama matsayinsu.
Mun kasance muna aiki tare kuma har zuwa yanzu babu wani sabani ko nuna bambanci, domin mukan zauna tare mu tattauna batutuwa da dama.
Sukan ba ni shawarwari kuma muna komai tare. Bayan ka zama Sarkin Kano, ka rika kai ziyara sassa da dama na kasar nan da jihohi daban-daban.
Ka kulla alaka da sauran sarakuna, amma wanda mutane suka fi mayar da hankali a kai, shi ne ziyararka a Ilori inda ka samu gagarumar tarbar da ta jawo hanalin mutane da dama, yaya wannan dangantaka take a yanzu?
Lokacin da ka zamo Sarki, hakan ya kunshi abubuwa da yawa. kamar yadda na sha fadi, shugabanci a wannan gida abu ne na ci gaba da tabbatar da al’ada da kula da ta’adu da kuma wasu abubuwa da suka haifar, kuma mun taso mun iske marigayi Sarki yana hulda ta girmamawa da sauran sarakunan wajen Kano har ma da na wajen Arewa. A cikin zukatanmu muna da yakinin wannan alaka ta yi amfani sosai ga kasar nan baki daya, musamman a lokutan rikici. Don haka idan muna da yakinin cewa abin da iyayenmu suke yi daidai ne, kuma sun kawo ci gaba mai yawa, ba mu da dalilin da ba za mu yi koyi da su ba.
Wannan ne ya sa ina zama Sarki nan take na fara kokarin yadda zan karfafa dangantakar Kano da sauran sassan kasar nan, musamman a wannan lokaci da al’amura suke tafiya a karkace, kuma mun gode Allah ziyarar ta ba mu damar ganawa da sarakuna da shugabannin addini da jami’an gwamnatoci har ma da sauran jama’ar kasa, inda muka zauna irin zama da jama’ar gari muka tattauna muka samu bayanai masu yawa da za su taimaka mana a kan gudunmawar da ta kamata mu bayar ga al’umma.
Idan muka koma kan batun Ilori, abu ne na matukar farin ciki da tunawa, nan ne mahaifiyarmu ta fito kuma muna daukar Ilori gidanmu. Don haka ban ji mamaki ba lokacin da na je can aka yi mini tarbar da kake magana a kanta. Kuma ba a Ilori kawai muka samu kyakkyawar tarba ba, duk inda muka je muna samun kyakkyawar tarba, kuma ina da yakinin ba don komai ba ne, face kyakkyawar dangantakar da iyaye da kakanninmu suka kulla.
Idan muna magana a kan Ilori, in ba domin mahaifinmu ya auri gimbiyar Ilori ba, hakika ba za mu samu abin da zai jawo maganar da muke yi a kan haka a yanzu ba. Don haka wadannan abubuwa da ka sani su ne muka dora a kai kuma muna cin gajiyar abin da suka shuka ne a lokacin da suke gadon sarauta.
Bambance-bambancen da kake magana yanzu suna fuskantar barazana inda ake ta karaji iri-iri, wadansu na kiran a sake fasalin kasa yayin da wadansu suke kiran a bari su kafa kasarsu. Me kake ganin ya kamata shugabanni su hadu su yi don magance wannan batu?
Lokacin da wani ya yi magana a kan sake fasalin kasa, me sake fasalin kasar yake nufi? Yana nufin mabambantan abubuwa ne ga mabambantan mutane. Ka tambayi mutanen Arewa da Gabas da Kudu da Yamma, za ka samu amsoshi mabambanta kana bin da sake fasalin kasa yake nufi. Don haka a tajaice wannan yana nuna akwai dimbin kidimewa a kan wannan batu na sake fasalin kasa.
Don haka abin da zan bayar da shawara, shi ne shugabanni da masu ruwa-da-tsaki su zauna su yi dubi da idon basira su nemo mafitar da za ta taimaki al’umma gaba daya ba daidaiku ba. Domin da dama wadannan matsaloli daidaikun mutane ne suka jawo su, saboda suna duba abin da daidaikun za su ci gajiya.
Ina da yakinin cewa Najeriya za ta fi zama mai dakin zama da karfi, idan muka ci gaba da kasancewa a dunkule. Kuma daya daga cikin manufofin zagayawar da muka yi ita ce, mu ga ’yan uwanmu maza da mata da suka fito daga wajen Arewa tare da kokarin karfafa dangantaka da ajiye bambance-bambancenmu wadanda kananan abubuwa ne idan aka kwatanta da abubuwan da muka hadu a kansu.
Don haka ina da yajinin yunkurin zai haifar da da mai ido kuma za mu ci gaba da tuntuvar masu ruwa-da-tsaki.
Duk lokacin da na je wata jiha, nakan gana da gwamnati da sarakuna kai har ma da jama’ar gari kamar yadda na fadi a baya. Mu tattauna bambance-bambancenmu don ganin yadda za mu magance su ba tare da rarrabuwar kai a tsakaninmu ba.
Kuma kamar yadda na fadi, a duk abin da za mu yi, wajibi ne mu yi da kyakkyawar niyya zuciya sake. Duk lokacin da aka tsarkake zuciya aka samu kyakkyawar niyya, Allah zai taimaka mana mu samu nasarar magance matsalolin da muke fuskanta.
A shekara biyu da suka gabata Jihar Kano da Masarautar Kano sun haxu da abubuwa da dama wadanda suka kai ga zamanka Sarkin Kano, yanzu wata 15 muna magana a kan bikin nadi, mene ne abu karshe ne da zai tabbatar maka da gadon wannan gado? Kuma yaya dangantakarka da dukkan jama’ar da lamarin ya shafa, kamar tsofaffin hakimai da mutanen da a da suke karkashin wannan masarauta amma yanzu suna wata masarauta?
Kafin a kirkiro sababbin masarautu muna tare da dukkan sababbin sarakunan shekara da shekaru, wadansu fiye da shekara 30. Bari in dalla-dalla, tun lokacin da na zama hakimi kuma mai rike da sarauta a 1990, dukkan sarakunan masarautun da aka kirkiro muna tare kuma muna da kyakkyawar dangantaka, muna girmama juna muna martaba juna sosai.
Kamar yadda na fada, rayuwa za ta ci gaba da sauyawa, idan ba ka tunanin canji a rayuwa zai zamo kana yaudarar kanka ne. Ta yiwu hanyar da canji zai zo ya sha bamban, ko kan yadda muke tunanin zai faru.
Don haka idan abu ya faru, tunanin yadda za ka tafiyar da shi a rayuwa ta yadda zai yi aiki ya amfane ku da kuma al’ummarku ne babban abin yi.
A wurina dangantakata da sauran masarautu da sarakuna har ma da jama’ar da suke karkashinsu, tana nan tana armashi ba mu da matsala, in baya ga yadda za su karbi umarni daga mabambantan masarautu a yanzu ba kamar a baya da babbar masarauta ita ce Kano.
Amma hakika dangantakar kyakkyawa ce kuma za mu ci gabada yin aiki don kara inganta ta don saukaka rayuwa ga daukacin jama’ar masarautunmu dabandaban.