Mato Yakubu, jarumin fina-finan Hausa wanda aka fi sani da Malam Nata’ala a shirin Dadin Kowa, ya nesanta kansa da wani bidiyon da ake yadawa a inda ake yabon Shugaba Buhari.
A hirarsa da Aminiya, Malam Nata’ala ya ce bidiyon da ake yadawa a shafukan sada zumunta tsoho ne da ya yi tun a shekarar 2015 a farkon mulkin Buhari, amma yanzu ya ba ya tare da shi.
- Najeriya za ta fara samar da fensir a cikin gida
- Kotu ta yi watsi da daukaka karar wanda ake zargi da wakar batanci a Kano
Dan wasan kwaikwayon ya ce a da shi dan ga-ni-kashenin shugaba Buharai da jam’iyyar APC ne.
Nata’ala ya ce ya yi wannan biyoyin ne a wancan lokaci don kare Shugaban Kasar, amma yin hakan bai amfana masa komai ba.
Malam Nata’ala ya ci gaba da cewa wasu ne suka dauko tsohon bidiyon a yanzu suke yadawa a matsayin kamfen don sun ga cewa lokacin babban zabe ya kusa, suke so su ci da guminsa.
“Yanzu zan yi wani sabon bidiyon in tsame kaina daga wancan tsohon bidiyon, sannan kuma zan yi Allah Ya isa ga duk wanda ya ke yada shi,” inji Malam Nata’ala mai sittin goma.
Dalilin janye goyon bayansa ga Buhari a cerwarsa, shi ne wahalar da talaka yake ciki a yanzu, da tabarbarewar tsaro da kuma sauran da wahalhalun da kasar ta ke ciki, baya ga watsi da aka yi da su duk da irin gudunmawar da suka bayar wajen kafa gwamnati.