Wani bidiyo dauke da bandir-bandir din ‘naira’ 2000 da kuma 5000 sun sake bulla a shafukan sada zumunta.
Sai dai bidiyon ya bulla karon farko a shekarar 2020 a cewar Mohammed Bello Abbass Dallawa, wani mai sharhi kan al’amuran yau da kullum kamar yadda bincikensa ya nuna.
- NAJERIYA A YAU: Yadda Sauya Takardun Naira Za Ta Shafe Ku
- Sauyin Kudi: CBN da Ministar Kudi sun sa zare
Shafin bin diddigi na labaran karya na Africa Check, ya bayyana labarin a matsayin na karya ne a ranar 20 ga watan Yulin 2021, inda kuma gano cewa wani shafi mai suna Oriental Times ne ya soma wallafa bidiyon.
Bangaren yaki da labaran karya na BBC shi ma ya gano cewar har yanzu shafin na aiki duk da cewar rajistar Oriental Times ya kare kuma suna shirin sayar da shi.
Bugu da kari, sashen binciken gaskiya na BBC Disinformation, shi ma ya bi diddigin bidiyon da a yanzun ake yadawa wanda wani mai suna @smartgabriel a shafin Tiktok mai mabiya 29,000 ne ya fara yada shi a ranar Litinin 24 ga Oktoban 2022.
Babban Bankin Najeriya CBN ya taba fitar da wani bidiyo mai tsawon dakika 30 a ranar 31 ga watan Mayu, inda ya musanta sahihancin wannan bidiyon na kudaden.
Sannan CBN din ya gargadi ‘yan Najeriya da cewa duk wanda aka kama shi da su zai fuskanci shari’a,sai dai har yanzu ana ci gaba da yada bidiyon jabun kudin a shafukan sada zumunta musamman a kwanan nan da Babban Bankin ya sanar da shirinsa na yi wa wasu takardun Naira sauye-sauye.