✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Bidiyon Dala karya ce tsagwaronta —Ganduje

Ganduje ya ce kirkirar bidiyon aka yi domin goga masa kashin kaji saboda siyasa.

A karon farko Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ya musanta bidiyon zarginsa da karbar rashawar Dala daga hannun wani dan kwangila a Jiharsa.

Ganduje ya ce saddabaru aka yi wa bidiyon da aka baza, shekara uku da suka wuce, inda a ciki aka gan shi yana karbar bandur-bandur na dala yana cusawa a cikin aljihunsa.

“Tabbas bidiyon bogi ne kuma muna kan bincike da wasu tsare-tsare ta karkashin kasa da ba za mu bayyana ba. Amma tabbas suddabaru aka yi wa bidiyon don a goga mana kashin kaji,” inji Ganduje.

Ya fadi haka ne bayan wani dan asalin Jihar Kano, kuma mai fafutka, Kabiru Sa’idu Dakata, ya tambaye shi kan yaki da gwamnatinsa ke yi da cin hanci da kuma inda aka kwano wajen binciko gaskiyar bidiyon dalar.

Kabiru Dakata ya yi tambayar ce a lokacin shirin da aka yi da gwamnan a Sashen Hausa na BBC, mai suna ‘A Fada A Cika’ da ke bibiyar alkawuran zabe da ayyukan gwamnoni.

Ya ce an kirkiri bidiyon dalan ne domin a bata masa suna don hana shi tsayawa takara, amma wadanda suka yi shi za su fuskanci hukunci.

“Tsagwaron karya ce saboda babu abin da ya fari. Makarkashiya ce aka shirya domin a hana ni tsayawa takara da cin zabe, amma na yi takarar kuma na lashe zaben. Amma wanna ba shi ne abun damuwa ba, babban abin shi ne za mu yi maganin.”

Ya ce, “Ko kai za a iya yi wa hotonka suddabaru a nuna ka kana yin wani abu da hannunka ko da kanka, ana yi. Mutane za su iya yarda da karya,” inji gwamnan.

Tun shekarar 2018 da aka fitar da bidiyon a jaridar intanet ta Daily Nigerian lamarin ya yamutsa hazo, inda ’yan Najeriya ke cewa ya kamata hukumar EFCC ta bi bahasin lamarin.

Bidiyon Dalar ta kai ga Majalisar Dokokin Jihar Kano kafa kwamitin bincikar lamarin da ya kai ga zuwa kotu.

Jami’an Gwamantin Ganduje sun yi watsi bidiyon cewa na bogi ne, har Gwamantin ta yi karar mawallafin Daily Nigeria, Ja’afar Ja’afar, wanda ya fitar da bidiyon ya kuma kekashe kasa cewa sahihi ne.