Shugaban Amurka, Joe Biden ya amince zai gana da takwaransa na Rasha, Vladmir Putin bayan tababa da tankiyar da ta kullu a tsakaninsu kan yunkurin mamaye Ukraine da Rashan ke yi.
Vladimir Putin da Biden sun amince sun amince za su gudanar da wani taro a tsakanin su muddin Rasha bata mamaye Ukraine ba domin rage tankiyar da ake samu da kuma kaucewa barkewar yaki.
- Abba Kyari ya maka Gwamnatin Tarayya a Kotu kan ci gaba da tsare shi
- APC ta dage babban taronta na kasa har sai abin da hali ya yi
Wannan na zuwa ne kwana guda bayan yunkuri na karshe na shiga tsakani da Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi na yayayyafawa wutar rikicin ruwa.
Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, ya ce a shirye Amurka ta ke ta yi duk abin da ya dace, don ganin ba a kai ga ba wa hammata iska ba.
Ya ce shugaba Biden ya fadi karara cewa a shirye yake ya gana da shugaba Putin a kowane lokaci, a kowanne irin tsari, idan har hakan zai hana yaki.
Haka kuma, wani babban jami’in gwamnatin Faransa ya ce bangarorin biyu ne za su bayyana lokacin da za a yi taron da kuma wurin gudanar da shi, yayin da ake saran ya kunshi masu ruwa da tsaki a kan rikicin Ukraine.
Wannan gagarumin ci gaba ya zo ne bayan da Amurka ta bayyana cewar, Rasha ta kammala duk wani shirin da ya kamata domin mamaye Ukraine, yayin da kasashen biyu suka zargi juna saboda musayar rokoki.
A wata hira da BBC, Firaministan Birtaniya Boris Johnson ya ce Putin na son haddasa yaki a Turai idan har ya mamaye Ukraine.
Rahotanni sun ce akalla mutane 500 suka shiga zanga zanga a Birnin Madrid da ke Spain domin nuna rashin amincewar su da yunkurin mamaye Ukraine.