Biyu daga cikin daliban Sakandiren Bethel Baptist sun shaki iskar ’yanci bayan sun tsere daga hannun ’yan bindigar da suka sace su makonni biyu da suka gabata.
Wani babban ma’aikaci a makarantar da ya bukaci a sakaya sunansa, shi ne ya tabbatar da hakan yayin zantawa da Aminiya a ranar Alhamis.
Bayanai sun ce daliban biyu da suka tsere wadanda ’yan uwan juna ne a halin yanzu suna samun kulawa a wani asibiti da ba a fayyace sunansa ba.
“Tabbas dalibai biyu sun kubuta daga hannun wadanda suka yi garkuwa da su,” a cewar majiyar.
Jami’in Hulda da Al’umma na Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna, ASP Jalige Muhammad, ya tabbatar da faruwar lamarin.
A cewar ASP Jalige, jami’an ’yan sanda sun tsinto daliban ne a cikin jeji kuma aka yi gaggawar mika su asibiti.
“Sun tsere daga hannun ’yan bindigar sannan jami’anmu suka tsinto su a cikin daji, inda suka mika su zuwa asibiti, a cewar ASP Jalige.
Ana iya tuna cewa, a ranar 5 ga watan Yuli ne ’yan bindiga sun kai hari makarantar sakandiren Bethel Baptist High School da ke Jihar Kaduna.
’Yan bindigar da suka kai hari sun sace dalibai fiye da dari a sakandiren da ke hanyar Kaduna zuwa Kachia a Karamar Hukumar Chikun da ke Kudancin Kaduna.
Rahotanni sun ce ’yan bindigar suna neman fansa ta naira dubu dari biyar kan kowane dalibi daya da ke tsare a hannunsu.