✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Benzema ya karya tarihin Raul a Madrid

Cristiano Ronaldo ne kan gaba a yawan ci wa Real Madrid kwallaye a La Liga.

Karim Benzema ya kwace kambun Raul Gonzalez da ke zaman na biyu a yawan cin kwallaye a gasar La Liga a Real Madrid a tarihi.

Ranar Laraba, Real ta doke Elche 4-0 a wasan mako na 21 a gasar La Liga a Santiago Bernabeu.

Marco Asensio ne ya fara cin kwallo, sai Karim Benzema ya zura biyu a raga duk a bugun fenariti, sannan Luka Modric ya kara na hudu

Benzema ya ci kwallo 230 kenan, shi ne na biyu a yawan ci wa Real Madrid kwallaye a La Liga, ya haura Raul mai rike da gurbin.

Cristiano Ronaldo, kyaftin tawagar Portugal shi ne kan gaba a yawan ci wa Real Madrid kwallaye a babbar gasar tamaula ta Sifaniya mai 311.

Yayin da Barcelona za ta kara da Manchester United ranar Alhamis a Europa League, Real ta rage tazarar maki 11 da ke tsakaninta da Barcelona ta daya ya koma takwas.

Real ta buga wasa da Elche ranar Laraba ne, bayan da ta je Morocco ta lashe Kofin Duniya na Kungiyoyi wato FIFA World Club Cup.