Wata bazawara mai kimanin shekara 27 da ke kauyen Shuwarin a karamar Hukumar Kiyawa ta kai bazawarinta mai shekara 37 kotu tana tuhumarsa da yi mata ciki, lamarin da ya sa kanen mahaifinta ya kore ta daga gidansa.
Bazawarar mai suna Amina Inuwa da ke garin Shuwarin ta ce bazawarinta mai suna Isa Ibrahim Kargo Gidan Baushe shi ne ya yi mata cikin lokacin da ya yi lalata da ita a bayan gidan mai a kan hanyar Dutse a gindin wani itacen gamji da ta ce ko a Lahira wannan gamji yana cikin wadanda za su yi mata shaida a gaban Allah.
Da take karin haske lokacin da alkali yake yi mata tambayoyi ta ce, Isa bazawarinta ne, tsawon shekara biyu yana zuwa wurinta tunda aurenta ya mutu a lokacin ma tana da ciki bayan ta haihu ne soyayyarsu ta yi nisa kusan duk danginta babu wanda bai san yadda alakarsu take ba.
Ta ce Isa ya je wurinta zance ya fi sau 360 kuma babu abin da yake gudana a tsakaninsu face soyayya irin ta ma’aurata lamarin da ya kai Isa yana daukarta ta raka shi unguwa shi ma wani lokaci tana yi masa waya ya zo ya kai ta unguwa idan bukatar haka ta taso.
Ta kara da cewa wata rana ya zo ya dauke ta ya ce za ta raka shi unguwa sun tafi ne ya tsaya a gidan man da ke hanyar zuwa Dutse kusa da kamfanin yin man kuli suka je gindin wani gamji suka yi lalata kuma a wannan lokaci ne ciki ya shiga.
Ta ce daga wannan lokaci Isa bai sake yin amfani da ita ba, kuma cikin da ta samu wata bakwai ke nan.
Bazawarar ta ce Isa ya jima yana neman hanyar da zai yi lalata da ita amma bai samu ba sai da ya yi dabarar cewa ta raka shi unguwa. Ta ce ba ta tsayawa da kowa in ban da Isa kuma kowa ya san su tare bayan da ciki ya bulla ne yake neman ya kaurace mata.
Ta ce ta samu kanta a cikin kuncin rayuwa sakamakon aukuwar hakan, inda ta bukaci gwamnati ta sasanta su da dan uwan mahaifinta, domin wannan lamari kaddara ce marar kyau ta same ta.
Bazawari Isa Ibrahim Kargo ya musanta zargin inda ya ce bai taba yin lalata da bazawarar tasa ba, inda ya ce ya yi bincike an ce masa tana da cutar kanjamau saboda haka ne ya kaurace mata ba don an ce masa tana da ciki ba.
Ya ce, a shirye yake ya rantse a kan lamarin, inda ya ce ta yi masa sharri ne kawai saboda tana sonsa domin ya jima yana son ta zai aure ta ba manufarsa zina ba kamar yadda ta yi masa kazafi.
Bayan sauraren bangarorin biyu, Alkalin Kotun Lardi ta Shari’ar Musulunci da ke Dutse, Malam Ibrahim Yusuf Harbo ya mika masu husumar ga ’yan sanda don su gudanar da bincike sosai a kan lamarin, inda ya ba su mako daya su dawo da masu husumar gabansa.