Kulob din Bayern Munich na Jamus ya ce ya shirya wasan sada zumunta a tsakanin kulob din Inter Milan da AC Milan na Italiya da kuma na Real Madrid na Sifen a bana. Kulob din ya ce wasannin za su gudana ne a watan Yulin 2016 a kasar Amurka a shirye-shiryen tunkarar kakar wasa ta 2016 zuwa 2017.
A wani jadawalin wasannin da kulob din ya fitar a ranar Talatar da ta wuce, an bayyana yadda kulob din ya shirya wasannin sada zumunta uku da zai buga a Amurka wanda ake kira International Champions Cup (ICC). A duk shekara ce kulob din Munich yake shirya wannan gasa, sai dai a wannan karon za ta gudana ne a Amurka.
Jadawalin ya nuna kulob din zai fara wasan farko ne da AC Milan a ranar 27 ga watan Yulin 2016 a Chicago sannan a ranar 30 ga Yulin kuma zai kara da na Inter Milan a garin Charlotte sai kuma a ranar 3 ga watan Agustan 2016 ya hadu da na Real Madrid a birnin New York.
“Ganin yadda muka samu nasarar bude sabon ofishinmu a Amurka ta sa muka shirya wasannin sawa zumunta a can don mu farantawa dimbin magoya bayanmu rai da ke zaune a can,” inji shugaban kulob din Karl-Heinz Rummeigge a wata takarda da ya sanya wa hannu.
A shekarar 2014 ma kulob din na Bayern Munich ya yi balaguronsa ne a Amurka a shirye-shiryen tunkarar kakar wasa ta 2014 zuwa 2015 sai dai a wancan lokaci kulob din bai bude ofishin dindindin a can ba kamar yadda ya bude a bana.
Bayern Munich za ta hadu da Real Madrid a watan Agusta
Kulob din Bayern Munich na Jamus ya ce ya shirya wasan sada zumunta a tsakanin kulob din Inter Milan da AC Milan na Italiya da…