Kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich ta dakatar da dan wasanta Sadio Mané, wanda hakan zai hana shi buga zagayen wasansu na biyu da za su kara da Manchester City a Gasar UEFA.
Hakan kuwa na zuwa ne bayan Mane ya fasa wa abokin wasansa, Leroy Sane, baki, a lokacin da suka samu wata takaddama a tsakaninsu.
“Sadio Mané ba ya cikin tawagar ’yan wasan da za su fafata a wasan da za a buga da TSG Hoffenheim a karshen makon nan.
“An dauki wannan matakin ladabtarwa a kan dan wasan ne saboda rashin da’a da ya nuna bayan wasanmu da Manchester City.
“Bugu da kari za a ci tarar dan wasan mai shekara 31,” in ji Bayern Munich a shafinta na intanet.
’Yan wasan biyu sun ba hamata iska ne a dakin sanya kaya, bayan wasansu da Manchester City, wanda Bayern Munich ta kwashinta a hannu da ci 3-0 a ranar Talata.
Sai dai daga bisani an sasanta har suka ba wa sauran ’yan kungiyar hakuri, ko da yake ana ganin wannan fadan zai iya janyo musu matsala.
Amma dai daga an gansu tare a ranar Alhamis suna atisaye bayan sun bai wa sauran abokanan wasansu hakuri.