Dakarun Rundunar Sojin Saman Najeriya na musamman da ke Birnin Gwari a Jihar Kaduna, sun ceto ’yan Chinan nan su bakwai da aka sace wata shida da suka gabata.
Rundunar ta sanar da hakan ne a cikin wata sanarwar da Kakakinta, Edward Gabkwet, ya fitar ranar Asabar.
- Gwamna ya sa a kama wadanda suka dafa abinci mara dadi a wajen ‘party’
- Sojoji sun kashe ’yan ta’addan Boko Haram 6 a Borno
’Yan ta’adda ne dai suka sace mutanen a watan Yunin 2022, lokacin da suke aiki a wani wajen hakar ma’adinai da ke Ajata-Aboki da ke gundumar Gurmana da ke Karamar Hukumar Shiroron Jihar Neja.
Sanarwar ta ce, “Dakarun runduna ta 35 sun gudanar da wani samame da daddare a kauyukan Kamfani Doka da Gwaska, inda suka kai farmaki kan ’yan ta’addan a maboyarsu.
“Hakan ya tilasta wa ’yan ta’addan guduwa suka bar ’yan Chinan da ma makamansu, sakamakon makaman sojojin da suka fi karfin nasu.
“Bayan samun nasarar farmakin, an kwaso ’yan Chinan zuwa asibitin sojojin sama da ke Kaduna domin duba lafiyarsu,” inji sanarwar.
Rundunar ta kuma ce Babban Hafsan Sojin Sama, Iya Mashal Oladayo Amao, ya jinjina wa Kwamandan rundunar ta Birnin Gwari, kan jajircewarsu wajen fatattakar ’yan ta’adda a jihohin Arewa maso Yamma, duk da hatsarin da aikin nasu ke tattare da shi.
A wani labarin kuma, Gwamnatin Jihar Kaduna, ta yaba da kokarin sojojin na ceto mutanen.
Kwamishinan Tsaro da Al’amuran Cikin Gida na Jihar, Samuel Aruwan, a cikin wata sanarwa ranar Asabar ya ce Gwamnan Jihar, Nasir El-Rufa’i ya bayyana farin cikinsa da jin labarin.