Rahotanni daga jihar Zamfara na cewa bayan tuban da rikakken dan bindigar nan, Bello Turji, ya ce ya yi da fadan da yake yi da sauran ’yan bindigan, rahotanni na cewa yanzu sun fara komawa Dajin Birnin Gwari da ke jihar Kaduna.
Wani mazaunin jihar ya tabbatar wa Aminiya cewa yanzu haka wasu daga cikinsu sun fara tashi daga dazukan Birnin Magaji da Zurmi na Zamfara, suna yin dajin na Birnin Gwari.
- HOTUNA: Sabon rikici ya barke tsakanin dakarun Iraqi
- Kusan duk mata na ajiye bidiyon tsiraicinsu a wayoyinsu — Safara’u
Dajin dai ya hada kan iyakokin jihohin Zamfara da Katsina da kuma Kaduna.
Kamar yadda ganau da suka nemi a sakaya sunansu suka ce, ’yan bindigar na fitowa da dabbobi ne bila adadin, inda suke yi batar da sahu a matsayin su makiyaya ne.
Hakan ya sa suke wucewa ba tare da samun wata tsangwama ba.
Majiyar da ta fito daga yankunan da suke wucewa a jihar Zamfara da Katsina ta ce yanzu Turjin ya fitine su da kai masu hari saboda ya fi su makamai, yana kashe na kashewa, wadanda kuma suka tuba yana barin su yayin da wasu ke yin hijira.
Muna tafe da karin bayani…