Ana zargin wasu makiyaya da kisan wani matashin manomi mai suna Muhammad Hassan a gonar mahaifinsa da ke yankin Karu a Babban Birnin Tarayya Abuja.
Kisan na zuwa ne bayan kwashe sama da shekara 10 suna takaddama da makiyayan da suke zaune kusa da gonar tasu.
- Ayyukan ta’addanci ba za su kare a nan kusa ba – Gwamnan Zamfara
- ’Yan bindiga sun sace Hedmasta a Neja, sun bukaci a basu N100m
Lamarin dai ya faru ne ranar Juma’a, 14 ga watan Janairun 2022.
Daya daga cikin yayyen mamacin, Ibrahim Hassan ya ce mahaifinsu ya fara noma a gonar tun shekarar 1984, sai dai tun kusan shekara 10 da suka gabata, makiyayan sun yi ta yi musu barna a gonar tasu lokaci bayan lokaci.
Ya yi zargin cewa tun a baya, makiyayin ya sha yin yunkurin kashe matsahi a lokuta da dama, inda ko a shekarar 2021 ma sai da ya yi wa Muhammad din mummunan rauni a hanu.
A kokarin hana barkewar, Ardon yankin, da hadin kan dattawan makiyayan sun kamo daya daga cikin wadanda ake zargin, kuma sun damka shi ga ’yan sandan Karu, inda ake ci gaba da binciken a kai.
’Yan uwan marigayin dai na kira ga gwamnati da ta hukunta dukkan wanda aka samu da hannu a kisan dan uwan nasu, sannan a biya su diyyar ran kisan.
Duk kokarin mu na jin ta bakin makiyayan ya ci tura.
A nata bangaren kuwa, ofishin Rundunar ’Yan Sanda reshen Karun ya ce suna nan suna bincike a kai.
Shi ma wani abokin mamacin da lamarin ya faru a kan idonsa da bai so a ambaci sunansa ba, ya shaida wa wakilinmu cewa makiyayan da suka yi aika-aikar su hudu ne.
Ya ce lokacin da abin yake faruwa, ya ji hayaniya, amma ko kafin ya karaso sun riga sun kashe shi kuma sun gudu.
Tuni dai aka yi jana’izar mamacin a yankin Nyanya da ke Abuja, kamar yadda adadin Musulunci ya tanada.