Bayan shekara 51 da kammala Yakin Basasar Najeriya, Gwamnonin yankin Kudu maso Gabas sun amince a fara binne gawarwakin mayakan Biyafara da suka fafata yaki da dakarun Najeriya.
Gwamnan Jihar Ebonyi, kuma Shugaban Kungiyar Gwamnonin yankin ne ya bayyana hakan yayin wani bikin addu’a a Abakaliki, babban birnin Jihar ranar Lahadi.
- Najeriya A Yau: Yadda kasafin kudin 2022 zai shafi rayuwarku
- Yadda iyaye ke zuwa kasuwa don neman mai auren ’ya’yansu
’Yan awaren Biyafara dai masu neman ballewa don kafa kasar Biyafara sun fafata yaki da dakarun Najeriya na kusan tsawon shekara uku, tsakanin 1967 da 1970.
To sai dai har yanzu akwai tarin gawarwakin mayakan yankin da dama da ba a binne ba, tsawon wadannan shekarun.
A cewar Gwamna Umahi, tuni ya umarci jagorancin Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) reshen Jihar da masu rike da sarautun gargajiya da su fara shirin bikin binnewar.
Ya ce sun yanke shawarar daukar matakin ne a yayin wani taronsu da suka gudanar kwanakin baya a Enugu.
Ya ce, “Yayin taron namu na Enugu, an yanke shawarar cewa wadanda suka rasu na bukatar bikin binnewa na musamman, kun san kuma ba na wasa da irin wannan batun.
A kan batun hare-haren da kungiyar IPOB take kai wa a yankin kuwa a ’yan watannin nan, Gwamnan ya yi Allah-wadai da shi inda ya ce sam babu hannun Gwamnonin yankin a ciki, sabanin yadda wasu suke zargi.
Umahi ya kuma yi alkawarin bayar da tukwicin Naira miliyan biyu ga duk wanda ya bayar da bayanan da za su kai ga gano maboyar maharan a Jiharsa, ba tare da an bayyana sunansu ba.