’Yan sanda sun kubutar da wani karamin yaro da ’yan bindida suka yi garkwua da shi shekara biyu da suka gabata a lokacin da ya je kiwon shanu a yankin Birnin Gwari na Jihar Kaduna.
Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Zamfara ce ta sanar da kwato yaron mai shekara 13 ta bakin Jami’in Hulda da Jama’anta, ASP Muhammad Shehu, ranar Laraba.
Ya ce, “’Yan sanda daga Sashen Dabaru na Musamman da ke sintiria a yankin Dansadau a Jihar Zamfara sun kubutar da mutum uku da suka hada da wani yaro mai shekara 13, kuma dukkanninsu ’yan asalin Jihar Kaduna ne;
“An kai su asibiti domin duba lafiyarsu kafin a yi musu sauran jawabai sannan a mika su ga iyalansu,” inji shi.
ASP Muhammad Shehu ya ce yaron da aka ceto ya shaida musu cewa a tsawon shekara biyu da ya kwashe a hannun ’yan bindigar, sun tursasa shi ya yi musu kiwon dabbobinsu.
Ya kara da cewa an ceto yaron ne tare da wasu mutum biyu da ’yan bindiga suka yi garkuwa da su daga kauyen Tumburku da ke Karamar Hukumar Giwa ta Jihar Kaduna.
ASP Muhammad Shehu ya bayyana cewa an ceto mutanen ne a kusa da Dajin Mashayar Zaki da ke Karamar Masarautar Dansadau a Karamar Hukumar Maru ta Jihar Zamfara.