Ministan Wutar Lantarki, Injiniya Sale Mamman ya ce za a kaddar da na’urorin samar lantarki daga iska mai karfin megawatts 10 da ke Jihar Katsina a wannan watan.
Za a kaddamar da aikin na Naira biliyan biyar ne kusan shekara 13 bayan fara shi a yankin Lambar Rimi, na Jihar Katsina.
- Miyagun Kwayoyi: NDLEA ta cafke Mata 102 a Kano
- Ba za mu yi sulhu da ’yan bindiga ba —Monguno
- Ya kamata sojoji su bi Boko Haram har maboyarsu —Majalisa
- An rufe makarantun sakandaren gwamnati a Neja
Ministan ya ce: “Gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta dukufa wajen ganin an kammala ayyukan da aka yi watsi da su.
“Aikin samar da lantarki mai karfin 10MW daga iska da za a kaddamar a cikin watan nan a Katsina ya kunshi turakun samar da lantarki 37.
“Wannan wani bangare ne na kokarinmu na zuba jari a bangaren makamashi na zamani,” inji sakon da ya wallafa ranar Alhamis a shafinsa na sa da zumunta.
Aikin dai ya faro ne a matsayin na Gwamnatin Jihar Katsina kafin daga baya ya zama na Gwamnatin Tarayya a shekarar 2007.
Abin da aikin ya kunsa
Ministan ya ce aikin ya kunshi sayowa, kafawa kuma hadawa da kula turaku 37 samar da karfin lantarki daga iska masu karfin 275.
Kowane turke na da na’urar raba wuta mai karfin 315KVA na 33KV da kuma 400V a matakin samar da wutar lantarki.
An yi wa injinan tsarin Kulawa da Samun Bayanai (SCADA) don tattara bayanai, lura da aiki da sarrafawa har ma da kulawa daga nesa.
Aikin ya kuma kunshi sanya taransfoma biyu masu karfin MVA 7.5 da kayan hadi.
Kwangilar aikin samar da lantarki daga iskar ta hada da gyara da kuma samar da kayan gyaran na tsawon shekara biyu.
Ya kuma hada da da gina layin isar da wuta na kilomita 23 na kilovolt 33 daga turakun iska mai karfin 10MW.
Akwai kuma layin daukar wutar da aka samar zuwa tashar mai 132/33kV ta kamfanin Transmission Company of Nigeria (TCN) kuma tuni an fara aikinta.
Daga tashar, akwai layin raba wutar mai 33kV mai tsawon kilomita 17 don hada shi da tashar 132/33kV TCN a Jami’ar Umaru Musa Yar’Adua da ke Katsina tare da fadada tashar ta 33kV.
Yadda aka fara
Shirin kaddamar da tashar da aka yi a 2020 shi ne karo na biyar da ake shiryawa ba tare da hakan ya tabbata ba.
Aikin da tun farko ke da wa’adain wata 24 daga shekarar 2005, Gwamnatin Gwamna Umaru Musa Yar’adua ta Jihar Katsina ce ta fara shi kafin gwamnatin tarayya ta karbe a 2007.
Amma shekara 13 ke nan ana kai-komon kafin aka kammala.
Gwamnatin Tarayya ta bayar da aikin ne ga wani kamfanin kasar Faransa, Messrs Vergnet SA, a 2010 a kan Fam 18,500,000 tare da N494 miliyan da wa’adin kammala aikin na watanni 24, wato shekarar 2012 ke nan.
Tsakanin 2012 da 2020, sama da sau shida ana sa lokacin kammalawa aka amma abin na gagara.
Aikin ya gamu da matsaloli da dama ciki har da sace injiniyansa, garkuwa da wani dan kasar Faransa, Collomp Francis, barna daga mutane, da tsarin aikin gwamnati da kuma dabbobi da suka addabe shi bayan an yi watsi da shi.