Bayan shekaru 11 kungiyar kwallon kafa ta AC Milan ta lashe gasar Serie A ta bana da maki 86.
Nasarar Milan na zuwa ne bayan ta doke Sassuolo da ci 3-0 a wasan ranar karshe na gasar da aka fafata a Yammacin ranar Lahadi.
- Manchester City ta lashe Firimiyar Ingila ta bana
- IPOB: ’Yan bindiga sun fille kan dan majalisa a Anambra
Milan dai na bukatar cinye wasanta da Sassuolo kafin ta iya daga kofin, yayin da babbar abokiyar hamayyarta, Inter Milan ta kare a mataki na biyu da tazarar maki biyu tsakaninsu.
’Yan wasan na Stafano Pioli sun jinjina kofin duk da nasarar da Inter ta yi 3-0 kan Sampdoria.
Olivier Giroud ne ya zira kwallo biyu a wasan kafin daga baya Frank Kessie ya ci ta uku duk a cikin minti 36 kacal da soma wasan.
Karo na 19 ke nan jimilla da Milan wadda ake yi wa lakabi da Rossoneri ta lashe babbar gasar Italiya ta Serie A a tarihi.