Bayan rahoton da Aminiya ta yi a kan tattakin da iyalan ‘yan canjin da aka tsare zuwa fadar Sarkin Kano, a karshe dai an ba su damar ganawa da mazajensu.
Aminiya ta ruwaito cewa iyalan ‘yan canjin sun je wajen Sarkin Kano Aminu Ado Bayero ne don kai kuka game da halin kuncin da suka shiga sakamakon tsare mazajensu da ‘yan uwansu tsawon wata 11 ba tare da gurfanar da su a gaban kotu ba.
- DAGA LARABA: Yadda labaran karya ke buya a tsakanin al’umma
- Yadda Afirka za ta ci moriyar fasahar samar da rigakafi
Maidakin daya daga cikin ‘yan canjin, Habiba Ibrahim Ladan, ta shaida wa Aminiya cewa mata da ‘yan uwan wadanda aka kama na tururuwa zuwa Abuja – inda ake tsare da su – don ganawa da su.
Halima Garo ma na cikin matan da suka tabbatar da cewa sun gana da mazajensu ido da ido.
“Mun gode wa Allah suna raye cikin koshin lafiya.
“Sai dai kawai suna cikin damuwa sannan sun rame, amma mun gode wa Allah”, inji ta.
Shi ma wani da aka kama dan uwansa wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce ya gana da dan uwan nasa, kuma yana cikin koshin lafiya.
Aminiya ta ruwaito cewa an shirya gurfanar da ‘yan canjin da aka cafke a kan zargin suna da hannu a daukar nauyin ta’addanci ranar 23 da 28 ga watan Fabrairu, da 1 ga watan Maris da kuma 8 ga watan Afrilun 2022.
Wasu daga cikin iyalan ‘yan canjin dai sun bukaci gwamnatin tarayya ta saki mazajensu da ‘ya’yansu ko kuma a gurfanar da su a gaban kotu.
Sun kuma bayyana yadda rashin gurfanar da su gaban kotu kamar yadda kundin tsarin mulki ya tanadar, ya sanya su cikin damuwa.
Idan ba a manta ba, ana tuhumar ‘yan canjin ne wadanda aka kama a sassan kasar nan daban-daban, da daukar nauyin ta’addancin kungiyar tada kayar baya ta Boko Haram.
Wasu daga cikin ‘yan canjin na harkokinsu ne a kasuwar canjin kudin da ke Wapa a Karamar Hukumar Fagge a Kano.