✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Bayan kwana 80 an sako ma’aikatan jinyar da aka sace a Kaduna

An bayar da fansar Naira miliyan 10 da babura da wayoyin salula.

Wasu ma’aikatan jinya biyu da aka sace a Jihar Kaduna, sun shaki iskar ’yanci bayan shafe kwanaki 80 a hannun ’yan daban daji.

Tun a watan Afrilun da ya gabata ne ma’aikatan jinyar biyu, Afiniki Bako da Grace, suka fada komar masu garkuwa da mutane yayin da suke aikin dare a Babban Asibitin Doka da ke Karamar Hukumar Kajuru a Jihar Kaduna.

Da yake tabbatar da kubutarsu, Shugaban Kungiyar Ma’aikatan Jinya da Ungozomai ta Kasa reshen Jihar Kaduna, Kwamared Ishaku Yakubu, ya ce an sako matan biyu na da misalign karfe 7.00 na yammacin ranar Asabar, 10 ga watan Yuli.

Ya ce babu wani karin kudin fansa da aka bai wa masu garkuwar doriya a kan Naira miliyan 10 da aka biya su tun farko.

Sai dai ya ce an bai wa masu garkuwa sabbin Babura biyu gabanin sakin matan biyu.

Aminiya ta ruwaito cewa, tun bayan sace ma’aikatan biyu da aka yi, an bayar da fansar Naira miliyan 10 da katin kiran waya na Naira dubu hamsin da kuma wayoyin salula hudu kirar kamfanin Techno.