✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Bayan kwana 55, Sanata ya kubuta daga hannun ’yan bindiga

Tsohon dan Majalisar Dattawa, Sanata Nelson Effiong, ya kubuta daga hannun masu garkuwa da mutane bayan shafe kwana 55 a hannunsu. Tsohon sanatan wanda ya…

Tsohon dan Majalisar Dattawa, Sanata Nelson Effiong, ya kubuta daga hannun masu garkuwa da mutane bayan shafe kwana 55 a hannunsu.

Tsohon sanatan wanda ya wakilici mazabar Akwa Ibom ta Kudu daga 2015 zuwa 2019 ya fada hannun masu garkuwa da mutanen ne a garin Uyo a ranar 5 ga watan Satumba, 2021.

Daga baya masu garkuwa da shi sun bukaci kudin fansa Naira miliyan 200 daga iyalansa, sai dai babu tabbacin ko an biya kudin fansa kafin a sako shi.

Sakataren Yada Labaran Jam’iyyar APC na Jihar Akwa Ibom, Nkereuwem Enyongekere, ya ce an sako sanatan ne a ranar Juma’a.