✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bayan kwana 105: Matasan Kebbi sun gano adadin kwayar gero da ke buhu

  Kidaya ta fito da masautar Yawuri a duniya – Sarkin Yawuri   Za a kai buhun geron Gidan Tarihi na Kaduna Gwamnati A ranar…

  •   Kidaya ta fito da masautar Yawuri a duniya – Sarkin Yawuri
  •   Za a kai buhun geron Gidan Tarihi na Kaduna Gwamnati

A ranar Asabar da ta gabata ce matasan Gungu a Yauri suka yi bikin kammala kirga buhun gero bayan sun shafe kwana 105 suna kidayar. Wakilinmu ya rubuta mana rahoto kan haka:

 

Yadda lamarin ya taso

A garin Yawuri da ke Jihar Kebbi akwai wata majalisa ta matasa wadda ke da zama a Gungu garkar Sarkin Yakin Sarkin Yawuri. Majalisar ta hada matasa 58 da ke zama duk bayan karfe 4 zuwa 7 na yammacin kowace rana inda suke tattauna al’amuran yau da kullum, kuma idan wani abu ya taso ga daya daga cikinsu sukan hadu domin taya shi murna ko bakin ciki.

Wadansu mutane suna yi wa majalisar kallon majalisa ce ta sada zumunci a tsakanin matasa da ke sassan garin Yawuri wadda ta faro daga unguwa inda ta fadada zuwa sassan garin Yauri, kuma bayan tattauna al’amura tare da zakulo wasu abubuwa masu muhimmanci domin wasa kwakwalwa da abin da ya shafi duniyarsu da lahirarsu, majalisar ta yi suna wajen kare mutuncin ’ya’yanta, wadanda kowanensu yake da sana’a ko aiki, kuma matasan shekarunsu na farawa ne daga 22 zuwa 35.

Muhawara

A ranar 26/06/2018, wata muhawara ta barke a tsakanin mazauna majalisar, inda daya daga cikinsu mi suna Safiyanu Muhammad ya jefa wata tambaya mai taken da buhun gero da motocin Najeriya wanne ya fi yawa? Sai wani ya ce, ba za a taba hada abin da ba a san adadinsa ba a matsayin bangaren muhawara, sai dai a dauki mutanen Najeriya tunda akwai kidaya da aka yi a shekarar 2006, kuma akwai hasashen wannan shekara ta 2018. Nan ne wadansu suka dauki buhun gero a matsayin bangaren muhawarar wadansu kuma suka dauki mutanen Najeriya, muhawarar ta yi zafi kowa ya ki saki abinda ya sa Yusuf Abubakar ya yanke shawarar kawo buhun gero don a kirga shi. Burinsa shi ne kawo a karshen muhawarar inda kowa ya amince. A ranar an tashi da raha daga bisani majalisa ta sayi buhun geron daga hannunsa ta ba shi kudinsa.

A ranar 29/06/2018 ne aka samu masu fara kirga geron abin da ake kallo shi ne irinsa na farko a tarihi. An kawo buhun gero aka gaba da kirgawa cikin natsuwa da raha, inda aka aje ranar Babbar Sallah a matsayin ranar ba da sakamako, sai dai hakan bai samu ba, har zuwa ranar da majalisar ta fara haskawa a duniya, bayan ziyarar da Muryar Amurka (BOA) ya kai wa majalisar, abin ya kara jan hankalin mutane da kafafen watsa labarai na Najeriya, kamar NTA da Daily Trust da Aminiya da Radiyon Albarka, Bauchi da Radiyon Jigawa da Freedom Kaduna da Whatsapp da Google da Twitter da sauransu. Wannan kirga ta ci gaba da jawo hankali da ra’ayin al’ummar duniya, kowa yana jiran jin sakamako har zuwa ranar Juma’a 11/10/2018 da aka kafa tarihin kammala kirgar wadda ita ce irinta na farko da aka taba yi a duniya baki daya. Bayan an shafe kwanaki 105 kafin a kammala wannan aiki na kirga.

Alfanun da ke cikin lissafin gero

Za a iya amfanuwa da kirgar gero da matasan suka yi ta fuska daban-daban, za a iya amfani da wannan kirga domin bunkasa noma da sanin adadin kwayar geron da aka shuka da sanin kkwaya nawa ake girba a kowace gona.

Masu kirga sun ce Najeriya a matsayin kasa da ke da arzikin noma za ta iya amfani da wannan kididdiga domin sanin adadin geron da aka girbe a bana da sanin geron da ake bukata a shekarar da ke tafe da ma duniya baki daya. Haka zalika za a iya amfani da tsarin da suka bi wajen kirga dukan nau’in hatsi da ake da su tare da bukansa ci gaban kasa saboda masana na cewa duk abin da ke da alaka da lissafi yana bude kwakwalwa.

Abin da buhun gero ya kunsa

Masu kirgar sun ce sun yi amfani da nau’in buhun geron da ake yi wa lakabi da Dan-Hausa ne geron dan asalin kasar Tambuwal ce gero kuma ana yi masa lakabi da inda ake noma shi kuma haka na da tasiri ga gero.

Sun ce geron yana da hasken tsaba da yanayin samar da abin da ake kira kullu (kamu) ko tuwon tsabarsa ya sa ake masa lakabi da sunaye daban-daban kamar Dan Hausa ko Dan Neja, sai dai ko bayan nau’in gero da aka yi gida biyu a kowane kashi akwai nau’i-nau’i da ake samu na gero masu bugun gero da dan Neja. “Mu kuma geron da muka yi amfani da shi shi ne Dan Hausa. Dan Hausa mun dauki dan kasar Tambuwal, gero ne mai haske da kuma manyan ido, gabanin lissafin mun yi amfani da sabon gero mai nauyin gaske ga haske ga sha’awa nauyinsa ya kai kilo 100 fatar buhu na da nauyin rabin kilo.

“Bayan mun kammala lissafi, mun sake auna buhun geronmu inda muka gano cewa geron ya rage nauyi da haske sosai inda ya koma kilo 94k fatar buhun tana nan da nauyin rabin kilo. Mun yi amfani da abin awo ko ma’auni kirar Ingila,” inji jagoran masu kirgar.

An dai kammla lissafi cikin makonni 15, kwanaki 105, sun samu ranakun aiki 99 da ranakun hutu 6 kuma sun yi kimanin awa 297.

Raba-gardama

Ma’aikata 37 da suka yi kwana 105 suna kidayar buhun gero sun samu kwara miliyan goma sha daya da dubu dari tara da saba’in da tara da dari takwas da sittin da takwas (11,979,868).

A ranar bikin Farfesa Aliyu Muhammadu Bunza na Jami’ar Tarayya da ke Gusau, ya gabatar da kasida mai taken: “Wurin da babu kasa nan ake gardamar kokuwa.”

Ya ce: “Matasan da suka shiga aikin su 37 ne domin su dace da ranakun mako, binciken ya dauke su kwanaki 105, kusan wata uku da kwana biyar a kan kidayan farilla, idan bai cika farilla ba wata uku da kwana takwas. Su 37 na nuna mana kisan baki sai taro, hannu daya ba ya daukar jinka. Idan aka ga cikas ga abin taro a bar zargin mutum daya matsalar kurar gardi ce, idan za a yi wata uku na kidayar buhun gero, to wata ko shekara nawa za a dauka na tantance matsalar da ke ga kowane kwano ko sa’i ko tiya?” “Kwatanta wannan da matsalolin kasarmu da mutanenta da jihohinta da yankunanta da kabilunta da addinanta da al’adunta kuma duk a ce mutum daya ne limaminta. Yaya za a yi ya kauce wa rafkanuwa?

A tunaninmu buhun gero ba ya kidayuwa kai-tsaye a samu hakikanin abin domin saninmu ne kwarorin gero kanana ne adadin da ke cika buhu ba su da iyaka. Wanda duk ya ce zai kidaye su ya baro jan aiki. Da wuya a samu katon da zai dora buhun gero a kansa shi kadai dole sai an aza shi. Ba a san namijin da ke rabin yini da buhun gero a kansa ba. Duk wanda aka dora masa shi aka sai an taru za a taya shi saukewa. To kwatanta wannan da yawan ’yan Najeriya da bukatocinsu da ke kan mutum daya kacal tsawon shekaru hudu.

Ta tabbata kwarorin gero 11,979,868 aka samu a buhu da aka kirga masana noma sun tabbatar da cewa, damin gero biyar ke buhu. Matsakaicin manomi na noma dame saba’in wanda zai ba da buhu 14. A cikin kowane dame ana samun kwarori 2, 395, 973, 6 manomi daya mai noma dami 70, buhu 14 buhunsa daya na ciyar da mutum 210 nomansa gaba daya zai ciyar da mutum 2,940.

Madalla da muhawarar matasa da ta buda mana kafar sanin kasarmu da shugabanninta da yadda za a iya wadatar da ita da kayan gona.”

Ya kara da cewa: “Ma’aikatanmu 37 da suka yi kwana 105 suna kidayar buhun gero sun samu kwara miliyan 11 da dubu 979 da 868. A ma’aunan buhu kashi uku yake kamar haka:

a. Babba mai mudu 70 tiya 35, kwarori a mudu 171,140.9

b. Matsakaici mai mudu 65 tiya 32.5 kwarori a mudu 187.305.6

c.  Karami mai mudu 60 tiya 30, kwarori a mudu 199.664.4

Diddigi

1. Mudu daya na ciyar da mutum 3 ci daya kacal

2. Buhu daya na ciyar da mutum 210 ci daya kacal

3. Mutum daya na bukatar mudu daya a yini ci 3 kacal

4. Buhu daya na ciyar da mutum 70 a yini ci 3 kacal

5. Yawan ’yan Najeriya 200,000.000 a raba da 70 = 2,857,142.857.

6. ’Yan Najeriya na cin buhun gero 952,380.9524 ci daya a wuni

7. ’Yan Najeriya na cin buhun gero 2,957,142.857 a wuni.

Sakamakon bincike

Muddin ta tabbata yawan ’yan Najeriya ya kai miliyan 200, dole hukuma ta zage damtse wajen inganta noma ta fuskar tallafa wa manoma, inganta ma’aikatun gona da fadada bincike a kan sha’anin noma.

Shugaban bikin Mai martaba Sarkin Yawuri Dokta Muhammadu Zayyanu Abdullahi a nasa jawabin ya bayyana cewa wadannan matasa 37 da suka kirga buhun gero ba karamar nasara ba ce ga masarautar Yawuri da Jihar Kebbi da kasa baki daya, domin kuwa tun da ake a duniya ba a taba samun wadanda suka kafa tarihi irin wannan ba sai matasan Yawuri, wannan ya sanya sun kara sanya Yawuri ta shiga cikin wani tarihi wanda ba a taba samun irinsa ba. Ya ce masarautar ta kafa tarihin zama masarauta ta farko da aka taba lissafa buhun gero a duniya, haka yake ga Jihar Kebbi da Karamar Hukumar Yawuri.

Ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta Jihar Kebbi su rika taimaka wa irin wadannan matasa ta hanyoyi daban-daban domin kara musu kwarin gwiwa.

Sarkin ya ce gwamnati ta zage damtse sosai wajen inganta harkokin noman rani ta fuskar tallafa wa manoma da kara ba da rance ga kananan ’yan kasuwa kamar yadda gwamnatin Jihar Kebbi ta fara a watannin da suka gabata.

A karshe Sarkin ya ce duk da cewa Kwamishinan Watsa Labarai na Jihar Kebbi Alhaji Mohammed Gado Marafa ya ce Gwamnatin Jihar ta sayi buhun geron a kan Naira dubu 500, ya ce a nasa tunani bai kamata a ce an sayar da shi ba, idan aka ce an sayar da shi an rage masa kima da daraja, kuma su ma matasan idan aka ba su kudin kimarsu za ta ragu, domin sun yi ne don masarautar Yawuri ta kafa tarihi.

A jawabin Gwamnan Jihar Kebbi Sanata Abubakar Atiku Bagudu wanda Kwamishinan Watsa Labarai Alhaji Muhammadu Gado Marafa ya wakilta, ya yaba wa matasan da suka kirga buhun gero domin sanar da mutanen Najeriya da buhun gero wa ya fi yawa.

Gwamnan ya ce lokacin matasan suka fara kirga buhun gero wadansu suna ganin kamar zauna-gari banza ne wadansu kuma su ce ba su da aikin yi, ashe wadannan matasa ba a taba samun irinsu ba a duniya sai a masarautar Yawuri a Jihar Kebbi, wannan ba karamar gagarumar nasara ba ce, ga Mai martaba Sarkin Yawuri da al’ummar Yawuri.

Gwamnan ya yi kira ga matasan Jihar Kebbi su jajirce wajen kirkiro ayyukan fasaha maimakon zaman kashe wando, kuma gwamnatin Jihar Kebbi a shirye take ta taimaka wa duk wanda ya kawo wani aiki na fasaha.

Bayan kamala taron wakilinmu ya zanta da Alhaji Muhammadu Gado Marafa, kan yadda za a yi da geron inda ya ce da farko gwamnatin jihar ta sayi buhun gero a kan Naira dubu 500, amma daga bisani Mai martaba Sarkin Yawuri ya ce ya ba wa Gwamnan kyautar buhun geron. “Saboda haka mun fara magana da Mai girma Gwamna a kan buhun, domin a kai shi gidan tarihi na Kaduna. Tun farko da gwamnatin Jihar Kebbi ta ce ta sayi buhun geron nufin gwamnati ta kai shi Gidan Tarihi na Kaduna, kuma nan gaba kadan gwamnatin za ta karrama matasan.