✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bayan kwana 102 jirgin farko ya tashi zuwa Abuja

Jirgin fasinja na farko ya taso daga Legas zuwa Abuja, bayan kwana 102 da rufe zirga-zirgar jiragen sama saboda bullar cutar coronavirus a Najeriya. Jirin…

Jirgin fasinja na farko ya taso daga Legas zuwa Abuja, bayan kwana 102 da rufe zirga-zirgar jiragen sama saboda bullar cutar coronavirus a Najeriya.

Jirin farkon ya bar filin jirgin sama na Legs ne da misalin karfe 7.15 na safiyar Laraba, ranar da Gwamnatin Tarayya ta bude harkokin sufurin jirage na cikin gida.

Rahotanni sun ce harkokin sufurin jiragen sama sun fara kankama a tashoshin inda ake sa ran jirgi na biyu zai tashi da misalin 11.00 na safe.
Hukumar Sufuruin Jiragen Sama ta Kasa (NCAA) ta amince da sake bude bangaren cikin kiyaye dokokin kariyar cutar COVID-19.

An fara da tashoshin Legas da Abuja ne a ranar Laraba 8 ga wata Yuli inda ake sa ran jirage uku za su tashi tsakanin Legas da Abuja daga cikin jiragen kamfanoni shida da NCAA ta ba wa izini.

Darekta Janar na NCAA, Kyaftin Musa Nuhu ya sanar da haka a taron da aka yi ta videoconferencing kan shirin dawo da harkokin jiragen saman.

A baya, Ministan Sufurin Jiragen Sama, Hadi Sirika ya ce a ranar 11 ga watan Yuli za a bude tashoshin jiragen da ke Kano da Fatakwal da Owerri da Maiduguri.

“Za a bude sauran tashoshin jirgin sama ranar 15 ga wata. Nan gaba za a sanar da na [jigilar] kasa da kasa”, inji shi.

Bayanan da wakilinmu ya samu daga kwamitin dake kula da bude filayen jiragen sun nuna dukkan kamfanoni da sauran masu ruwa da tsaki sun tanadi abubuwan da ake bukata daidai gwargwado domin fara gudanar da harkokinsu.