✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bayan kai masa hari, Gwamna Ortom ya yi ganawar sirri Buhari

A ranar Talata Gwamna Samuel Ortom na Jihar Binuwe, ya yi wata ganawar sirri da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a fadarsa ta da ke Abuja.…

A ranar Talata Gwamna Samuel Ortom na Jihar Binuwe, ya yi wata ganawar sirri da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari a fadarsa ta da ke Abuja.

Ganawar na zuwa ne kwanaki kadan da wasu ’yan bindiga suka kai wa gwamnan hari a karshen makon da ya gabata.

A ranar Asabar ce ’yan bindiga suka kai wa ayarin motocin gwamnan hari yayin da yake dawowa daga gonarsa a kauyen Tyomu da ke kan babbar hanyar Makurdi zuwa Gboko.

Bangarori da dama a kasar sun yi ta Allah wadai da harin, inda Shugaban Kasar a ranar Lahadi ya bai wa hukumomin tsaro umarnin gudanar da bincike mai zurfi a kan lamarin.