’Yan bindiga sun kashe akalla mutum 10 a Karamar Hukumar Sabon Birni ta Jihar Sakkwato, sa’o’i kadan bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya umarci sojoji su yi amfani da karin makamai wurin murkushe bata-garin.
Wani mazaunin garin Sabon Birni ya shaida wa Aminiya cewa maharan sun yi aika-aikan ne a wasu kauyuka da ke yankin Unguwar Lalle.
- Daga Laraba: Auren Wuf: Tsakanin soyayya da son kai
- Yadda aka yi jana’izar Sani Dangote, kanin Aliko Dangote
Ya ce ’yan bindigar sun kashe wani mai suna Abdullahi Usman a garin Unguwar Lalle, mutum tara a Tsangerawa da wasu mutum hudu a akauyen Tamindawa.
Sun kuma bude wa wani babur mai kafa uku wuta a kauyen Gajid inda suka kashe mutum uku nan take, mutum biyar da suka samu raunin harbin bindiga kuma ana jinyar su a asibiti.
Maharan sun kuma yi garkuwa da mutum uku a wani kauye, amma sun sako mutanen bayan kwana biyar da aka biya kudin fansa Naira miliyan biyu.
Amma Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Sakkwato, Kamaluddeen Okunlola, ya ce mutum takwas ne aka kashe, yana mai alkawarin daukar mataki a kan maharan.
“Sun kai harin ne a wasu kauyukan da ke wajen gari da ba za a iya zuwa cikin sauki ba saboda rashin hanyoyi masu kyau.
“Amma da yardar Allah za mu cim musu, abin da muke kokari ke nan.