✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bayan dakatar da hakar ma’adanai a Zamfara

A shekarun bayan Jihar Zamfara ita ce jihar da ta fi kowace jiha a Najeriya zaman lafiya. Duk inda ka ji sunan Jihar Zamfara, za ka…

A shekarun bayan Jihar Zamfara ita ce jihar da ta fi kowace jiha a Najeriya zaman lafiya. Duk inda ka ji sunan Jihar Zamfara, za ka ji wani abin alheri ne ake tattaunawa a kan jihar. Sai dai kash! A ’yan shekarun nan abin ya sauya kwata-kwata duk inda ka ji labarin Zamfara za ka tarar abin assha ne ke fuskantar jihar, ka ji an kashe ko an sace dukiyoyin al’umma ko an yi garkuwa da wani abin har ya kai ana kone dukiyoyin al’umma da shafe kauyuka a doron kasa.

Hakan ya sa da dama kauyukan Jihar Zamfara yanzu sun zama kangaye, noma ya tsaya cik! Makiyaya sun yi hijirar dole da ’yan shanun da suka rage musu.

Duk da wannan aika-aikar da ake yi mahukuntar jihar, sun yi kunnen uwar shegu da al’ummarsu. Kullum ba su da aiki sai shirya yadda za su rayu har abada kan karagar mulki. Ana labewa da kargo ana ci gaba da harbin barewa ta hanyar kokarin dora wadanda suka tabbatar za su yi musu biyayya sau-da-kafa da  kokarin kakkafa wadanda suka san ba su kware musu baya. Da ma ’ya’yansu tuni suka dora su inda suke son su jagoranta.

Duk lokacin da aka yi wani mummunan kisa na fitar hankali, in mun yi sa’a ne za mu ji maganar gwamnatin jihar. Kuma a madadin jaje ko tallafi ga wadanda abin ya shafa ko daukar matakin da ya dace, sai dai ka ji Gwamnan da makarabansa sun yi zama da ke kira na tsaro. Madadin su fito da hanyoyin daukar matakin da ya dace, sai su buge da daukar matakan da za su kara jefa talakawan jihar cikin mummunan halin da kan jefa wadansu daga ciki fadawa cikin aikin assha!

Abin mamaki Shugaba Buhari shi kansa da talaka yake da aminci da yarda gare shi, ya biye musu ta hanyar zura wa Zamfarawa ido ana yi mana kisan kiyashi.

Hasali ma matakin da Rundunar Sojin Najeriya ta dauka na kaddamar da rawar dajin da ta kira ‘Operation Sharar Daji’ da Shugaba Buhari ne ya kaddamar da shi a Zamfara, sai ya zama tamkar na banza, domin ba wani takamammen tasiri da ya yi. Mu al’ummar Jihar Zamfara muna ganin cewa, an dai nuna mana akwai jami’an tsaro ne da kayan aiki a Najeriya domin ba mu ga alfanunsu ba.

Sai dai alhamdulillahi bayan gangamin da muka yi a jihohin Kaduna da Sakkwato da Abuja domin nuna bacin ranmu kan yadda Shugaban ya nuna halin ko-in-kula da mu a ranar Asabar 6-4-2019, sakonmu ya isa ga Shugaba Buhari ya fara daukar mataki. Matakin da ya dauka shi ne dakatar da hakar ma’adanai a Jihar Zamfara.

Hakika wannan mataki ne mai kyau, kuma tun baya mun dade muna hasashen hakar ma’adanan da ake yi a jihar na daga cikin dalilan kisan kiyashi da ake yi wa Zamfarawa. Ko ba komai akwai tarin alamomin tambaya a kan masu hakar ma’adinan. Domin duk masifar da ake yi a jihar, ba ka taba jin an taba masu hakar ma’adinan.

A jihar har almajirai masu bara da kwargo da tsofaffi masu aikin gona a biya su da kananan ’yan kasuwa an yi garkuwa da su. Yayin da masu hannu da shuni har bibiyar rayuwarsu ake a cikin alkaryu don sanin duk wani motsinsu tare da sace su duk lokacin da dama ta samu. Amma duk da dimbin kudin da masu hakar ma’adanai suke samu, suna cikin dazukka kullum hankalinsu kwance ba mai taba su.

Shin me ya sa ba a yin garkuwa da su? Shin kudi ne ba su da su?  Me ya sa ba a kisansu?

Na san dai suna da jami’an tsaron da ke ba su kariya. Amma ko kusa wadannan jami’an tsaron ba su iya ba su kariyar da za ta hana a taba su.

Don haka muna matukar maraba da wannan mataki, kuma ya kamata a tsananta bincike a tsakanin masu wannan harkar, wannan ke nan!

Sai dai wani hanzari ba gudu ba, a sani ko alama wannan mataki kurum ba zai yi tasiri wajen farfado da al’ummar Jihar Zamfara su dawo cikin hayyacinsu, ba.

Don haka abin da za a yi shi ne; a tabbatar an yi binciken kwakwaf don gano masu hannu a wannan kisan kiyashi, tun daga masu daukar nauyinsu, kawo masu makamai da wadanda ke daure musu gindi.

Abu na gaba shi ne al’ummar Jihar Zamfara na bukatar karin jami’an tsaro da kayan aikin da za su fatattaki wadannan batagari, ba wai ta hanyar karfi kurum ba, har ta hanyar kwarewa da dabaru na musamman.

Sai kuma maganar dora jihar a kan tafarkin da za ta dawo kan ganiyarta, ta hanyar daidaita al’amura. Domin an samu dubban mata da suka zama gwaggware da yara marayu da aka yi wa iyayensu kisan gilla wadansu a gaban idonsu. A Zamfara baki daya babu matsugunin ’yan gudun hijira daya da aka killace wadannan yara ana kula da su, haka ya sa sun fantsama cikin manyan garuruwan Zamfara suna barace-barace don neman abincin da za su ci. Don haka dole a taimaki wadannan yara, a dora su kan tafarkin da za su rayu domin amfanin kansu da jihar baki daya. Wallahi muddin aka zura wa wadannan yaran ido, za a wayi gari su zama wata annoba ta musamman in sun girma.

Haka dole a nemi hanyar da za a samar wa matasan jihar makomar da za su dogara da kansu, domin shekara takwas aka yi a jihar ba a daukar aiki daga gwamnatin jihar ko bude wa matasan hanyar koyon sana’o’in hannu ba. Hakan ya sa an tara matasa da dama da suka kammala makarantu babu aikin yi, ba maganar wadanda ba su karatu ake yi ba. Wanda hakan ya taimaka matuka wajen haifar da wasu miyagun ayyuka a Zamfara.

Abu na karshe dole ne a sake gina kauyukan da aka tarwatsa.

Muna rokon Allah Ya sa kokenmu ya kai ga kunnuwan wadanda muka yi dominsu, kuma Ya ba su ikon share mana hawaye. Ya Allah! Ka bai wa jami’an tsaronmu ikon murkushe batagari a Jihar Zamfara da Najeriya baki daya.

 

Abdulmalik Sa’idu Mai Biredi, Tashar Bagu, Gusau (Jami’in Hulda da Jama’a na Kungiyar Muryar Talaka ta Kasa Reshen Jihar Zamfara) 08069807496.