Kwanaki sun rare
Ana ta harare-harare
Harara garken ’yan tamore
Ko a ce ’yan tabare
takaddamarsu ta kakare
Lamarin tamkar a duhun dare
An tafka kuskure
Ai ta-maza a daure
Har mu samu a murmure
Mu daina yi wa juna terere
Ai ilimi da tsare-tsare
kasarmu ta ketare
kabilu kar su kebanta da yare
A watsattsake a samu kwararre
Ko masanin kimiyya da kere-kere
Kowa ya daure
Laifukan juna a hankure
Mu kauce wa yin kure
Illolin baya an jure
Yanzu a bar yi wa juna ature
Wasu na kiran a ware
Haurobiyawa na son a warware
Kyakkyawan fage a share
Yadda kowa zai more
A daina dubin juna a harare
Harsuna an yi musu gantsare
An cefanar a cinikin furfure
Turawa sun koya mana kobare
Bokokon kobare-kobare
Gayu na ta gantsare-gantsare
Ma’anar ilmu za ai wa faskare
Famfarar fikar farare
Birgimar bugun bagun bagire
Farin farawar firamare
Sai a sako dalibai su dire
Jam’in jama’ar Jumare
Jan bijimin fullo are-are
Garken nagge an makare
Karsana an bi an sure
An ce ‘war-mi-ware’
Da can muna tare
kabilu sui tarayya a tattare
Babu suka da sare-sare
ba bare
Balle karyar kire
Mui ta zaurancen zaman zaure
Zantuka sun zurare
Tunkurar turara turare
Wuta aka hura da kirare
Jin dumin dadin gyare-gyare
Babban mutum mai rawani
Shi ke karbo umarni
In Bature yai izini
Don gyara karkara da birni
Bibiyar al’umma dama da hauni
Sai miyagu suka tubure
Magabta a sandare
Cin kwalar juna a makure
A bi a hankali Malam Ba’are
Anai maka harin hare-hare
Haure-hauren haure
Karairayar kare-kare
Curin cure-cure
Za a sa al’umma ta sankare
Da dungurin dungure-dungure
Gwaurikikin gwauron gwagware
Tunzurar tuzurun tuzurai
Muzuran muzurun muzurai
Kwaramniyar kwanare
A gangaren gara gare-gare
Turmi turakar tabare
Ango an rarumo aure
Amaryar na rangwadar amare
Farfajiyar gida tar a share
Fitilu sun haske wurare
Baturen Hawan-sa
Turawa ba wasa
Hausawa na ta sa-in-sa
Ginin hauhawar hawan-sa
Inda aka horar da ’yan kasa
Rumbun ilimi
Cike da watsattsaken malami
Na tawada da alkalami
Aiki ne muhimmi
Lallai a kara kaimi
Malam Bature
Da ya zo daga Turai
Yana sane sarai
Ya sanya mu ture-ture
Jahilai aka bar su a takure
Tuntuben tunburkai
Tunkuyin tumakai’
Lafkewar langabu lakakai
Soshe-soshen kaikai
Awon igiyar awakai
Mun yasar da ta’adun da
Muna ta sukuwar danda
A wajen aiki mui ganda
Mun daina kirgen kalanda
An dai karke da gada-gada
Kowa ya karkata akala
Ai yunkurin fita matsala
Domin zamani ya lula
Ka da kowa yai kasala
Illar lalaci ta fi zafin bulala
Mui aiki tukuru
Yadda kowa zai karu
Hankulanmu su tattaru
Mun fasko masu huda garu
Suna ta carar zakaru
An fasko kangararru
Abokan fandararru
Wai su ga gagararru
Sun yi shigar sunkuru
Suna tai mana dabarbaru
Masu zilliyar kadangaru
Suna ta sauya suturu
Tabaron Turancin tukururu
Da fuffukar tantabaru
Kun dai gani kuru-kuru
Karatun koyi ka koyar
Ya zam koyi ka kautar
Kwashi ka karkatar
Karbi ka kifar
Ko kwalfi ka kwararar
Talakawa
Sun gajiya da musgunawa
Ta-molar casawa da lallasawa
Artabun salansar sansanawa
Rafkanannun rukukin rafkanuwa
Tabarar tabarbarewa
Tanbadaddun tambadewa
Takurar tokarewa
Tattalin tulun tuttulewa
Tabargazar tabewa
Bakake da farare
Ka da kowa ya fandare
Boko ya tattare
Allon da aka saro a kututture
Karatu ne dai aka karkare
’Yan lalle
Nagartar ayyuka a daddale
Adon gari ban da shargalle
Ku ne dai sha lele
Ku dora mana sanwar kulele
Ko kiranye muke waTurawa
Mu lura da Larabcin Larabawa
Da farin cikin Faransawa
Jarumtar jaruman Jamusawa
Birgimar burgar Birtaniyawa