✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Batun Maku na ingancin zabe: Sallah daga liman take lallacewa

Babbban gibin da ke tsakanin talakawan kasar nan da masu mulkinsu a kowane mataki, bai wuce sadarwa ba. Abin nufi, a tawa gajeruwr fahimtar, su…

Babbban gibin da ke tsakanin talakawan kasar nan da masu mulkinsu a kowane mataki, bai wuce sadarwa ba. Abin nufi, a tawa gajeruwr fahimtar, su masu mulki sukan fadi dukkan abin da ransu ya yi masu dadi, su kuma tsaya kai da fata, lallai-ilallah sai talkawan su yarda da su cewa abin da suka fadi din gaskiya ne, don haka dole talakawan su saurare su, kuma su amince da su, ba tare da sun ce ga inda ya kamata a gyara, kai ka ce ba mulkin dimokuradiyya ake ciki ba, wanda ya tanadi `yancin fadin albarkacin baki, kamar yadda sashi na 38, na kundin tsarin mulkin kasar nan na shekarar 1999, ya tanada. Maimakon masu mulkin su fadi abin da ransu ya raya masu a zaman giyar mulki,su bar talakawa su amince ko kar su amince da su, amma an wayi gari a kasar nan duk wanda ya mayarwa da shugaba martani, an ci gaba da daukarsa dan adawa. Tsarin tafiyar da mulki irin wannan ba karamin wawan gibi yake haifarwa ba, tsakanin masu mulki da talakawa da suke mulka a kasar nan.    
Abin da ya san na ce haka, bai wuce irin yadda a kwanakin baya aka ji shugaban kasa Dokta Goodluck Jonathan yana kokawa da cewa wai kafofin yada labaran kasar nan sau tari suna amfani da jawabansa wajen bata gwamnatinsa. Kai! Ka ji mai karatu, a zaman mutum shugaba a cikin Iyalinsa ko a al`ummarsa, ya ci a ce kafin ya buda baki ya yi magana, ya zan ya tautauna abin da zai ce, don ko ba komai masu iya magana kan ce “Magana zarar bunu,” ma`ana idan ta fito baka iya mayar da ita. To ina ga maganar shugaban kasa irin na wannan kasa mai mutane sama da miliyan 160, wadda tafi yawan al`umma adaukacin nahiyar Afirka, da bambancin addini da na kabila da na jinsi da sauransu. Ka ga ya ci a ce a dukkan lokacin da shugabanmu za su yi magana ya rika sara yana duban gatari. Amma mu sau tari ba ka jin wasu muhimman jawabai daga Shugaba Jonathan sai in ya fita zuwa kasashen waje, ko kuma ya shiga wata majami`a.
Shi ma Ministan yada labaru Mista Labaran Maku kusan haka yake, sai ya cabo dukkan irin maganar da ransa ya raya masa ya fada wa talakawan kasa, ya kuma nemi lallai sai talakawa su amince. Alal misali dauki jawabin da ya yi a Hedkwatar Radiyon tarayya ta kasa da aka yi wa lakabi da Radiyo House da ke Abuja, ranar Juma`ar da ta gabata, lokacin da yake jawabi wajen kaddamar sababbin zababbun shugabannin `yan kwamitin zartaswa na Cibiyar hulda da jama`a na kasa baki daya. A wajen, an ruwaito Ministan yada labarai wanda kuma shi ne Mirista mai kula da Ma`aikatar tsaro, yana cewa a gwamnatin tarayya kadai ake samun ingantace kuma sahihin zabe mai cike da adalci.
“A yau ba sai gobe ba, ba wata jiha a kasar nan da ake gudanar da sahihi kuma ingantaccen zabe,” in ji Minista Maku, inda ya kara da cewa kusan makonni biyu da suka gabata, an yi wani zabe a wata jiha, (duk da dai bai ambaci jihar ba,  amma ana kyautata zaton da jihar Yobe yake), inda duk wanda ya ci ya fito ne daga  jam`iyyar da take mulki. Ya ci gaba da cewa “A kaddara mun gudanar da zabe a gwamnatin tarayya, kuma jam`iyyar da ke kan mulki ta lashe komai, duk kasa za a yi ca… tamfar za a yi yaki, amma mutane za su zauna a jihohi su rika kiran kansu`yan gaba-dai-gaba-dai, su gudanar da zabubbuka a jihohinsu, kowa ya ci daga jam`iyyarsu, kuma babu wani laifi akan haka.”
Wadannan su ne kalaman Minista Mista Labaran Maku akan yadda ake gudanar da zabubbukan Majlisun kananan Hukumomi a kasar nan, zabubbukan daga dukkan alamu sun tsone wa gwamnatin tarayya idanu, batun da a bisa ga gaskiyar al`amari haka yake, don kuwa duk kasa ana kokawa da irin yadda Hukumomin zabe masu zaman kansu na jihohi suke gudanar da zabubbukansu, ta yadda kamar yadda Ministan ya fadi a kowace jiha jam`iyyar da ke kan mulki ita take lashe dukkan mikaman da aka yi takara, tun daga kan mukamin Kansila zuwa na Shugaban karamar Hukuma, sai illa nadiran a wasu jihohi.
Amma ai masu iya magana kan ce “Sallah daga liman ta kan baci,” Dukkan wanda ke biye da yadda ake gudanar da zabubbukan kasar nan tun daga shekarar 1999, da aka dawo kan mulkin farar hula ya san cewa zabubbukan 1999 ne kadai aka yi cikin kamanta gaskiya da adalci, ya kawo jam`iyyar PDP, akan karagar mulki, sauran jam`iyyun adawa na wancan lokacin irin su AD da APP, su ma suka samu nasu rabon. Wasu daga cikin abubuwan da suka sanya aka gudanar da wancan zabe na shekarar 1999, cikin kamanta gaskiya da adalci da takai kusan dukkan `yan kasa sun amince da zaben, sun hada da irin hadin kan da aka samu daga akasarin jiga-jigan `yan siyasar kasar nan da a lokacin suka yadda suka shiga cikin jam`iyyar PDP, wadda a tarihin kasar nan aka hadu a inuwa daya da wadanda nasu taba shan inuwar siyasa daya, haduwar da aka yi da aniyar an gaji da mulkin soja na shekaru 16, ba kakkautawa (1983 zuwa 1999)
Kowa ya sani har da shi kansa Minista Labarar Maku zabubbukan da suka biyo bayan na 1999, wato na 2003 dana 2007 dana 2011, duk zama suka rika yi gara na jiya da yau akan lalacewa, ba don komai ba, sai don irin yadda jam`iyyar PDP da jiga-jiganta da suke mulkin gwamnatin tarayya suka rika mayar da zabubbukan tamfar a mutu ko a yi rai, al`amarin da ya kai saboda sanin yadda jam`iyyar ta PDP ta fara kwarewa a cikin iya kama-karya da murdiyar zabe da jin dadin mulki, sai da Yarima bicent Ogbulafor lokacin yana kan karagar mulkin shugabancin jam`iyyar ta PDP na kasa baki daya da giyar mulki ta kwasheshi ya ce PDP, za ta yi mulkin kasar nan har shekaru 60, masu zuwa.
Ya kamata masu mulki irin su Ministan yada labarai su sani, kamar yadda na fadi tun farko “Sallah daga Liman take baci,”sai har jam`iyyar PDP mai mulkin gwamnatin tarayya ta tsaya ta kimtsa gidanta, ta hanyar kamanta gaskiya da adalci a cikin dukkan harkokin gudanar da mulki da na siyasa a kasar nan, kana gwamnatocin jihohi da sauran `yan kasa su ma za su kamanta, amma muddin ta tsaya akan yin kama karya iri-iri, kamar yadda yanzu ake dauki ba dadi tsakanin jam`iyyar da wasu gwamnoninta, harkokin dimokuradiyya za su dagule.