✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Batun Maina ya dauki sabon salo

Akwai alamun Shugaba Muhammadu Buhari zai aike da sammaci ga Atone-Janar na Kasa, Abubakar Malami da Ministan Harkokin Cikin Gida, Abdulrahman Dambazau kan dawo da…

Akwai alamun Shugaba Muhammadu Buhari zai aike da sammaci ga Atone-Janar na Kasa, Abubakar Malami da Ministan Harkokin Cikin Gida, Abdulrahman Dambazau kan dawo da Maina aiki.
Aminiya ta gano cewa rahoton da Shugabar Ma’aikatan Gwamnati, Misis Oyo-Ita ta gabatar ga Babban Shugaban Ma’aikatan Shugaban Kasa, Abba Kyari ya nuna alamun za a nemi karin bayani daga wurin Malami da Dambazau.
Babban Mai Taimaka wa Shugaban Kasa kan Harkokin Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Malam Garba Shehu a sakon kar-ta-kwana da ya tura wa wakilinmu jiya da dare ya ce ana nazarin rahoton da Oya-ita ta mika.