✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Batun cewa Shugaba Jonathan hamshakin attajiri ne

A kwanakin baya ne wata kafar watsa labarai ta intanet a Amurka, Rich Lifestyle ta tsokano gidan rina, inda ta buga wani labari na abin…

A kwanakin baya ne wata kafar watsa labarai ta intanet a Amurka, Rich Lifestyle ta tsokano gidan rina, inda ta buga wani labari na abin da ta kira sunayen shugabannin kasa 10 da suka fi yawan dukiya a Afirika. Ta bayyana cewa Shugaban kasar Najeriya, Goodluck Jonathan da cewa shi ne na 6 a yawan dukiya, inda ya mallaki Dala miliyan 100. Labarin nan ya bata wa fadar Shugaban kasar rai, inda har aka jiwo mai magana da yawunsa yana kumfar baki, cewa idan wannan kafa ba ta janye labarin ba, to za su maka ta kotu domin neman hakki. Mai Magana da yawon Shugaba Jonathan, Reuben Abati, ya fitar da wata sanarwa, inda ya bayyana labarin da cewa “na kanzon kurege ne, marar hujja. Kamar yadda kowa ya sani, Shugaba Jonathan bai taba yin kasuwanci ko sana’a ba, duk tsawon rayuwarsa ya kasance ma’aikacin gwamnati.” Haka Abati ya ci gaba da bayani, yana fayyace bayanan yadda Jonathan yake rike da madafun iko tun daga 1999, kuma cewa bai da wata kafar samun kudi da ta wuce albashi da alawus-alawus a matsayinsa na Mataimakin Gwamna zuwa Gwamna, zuwa Mataimakin Shugaban kasa da kuma yanzu da yake Shugaban kasa.

Bayanan nasa sun ci gaba da cewa, wancan labari, an dasa shi ne da nufin bata sunan Jonathan, don a rika kallonsa a matsayin shugaba barawo, da nufin harzuka al’umma su kyamace shi. Duk da wadannan bayanai na Abati, har yanzu ba su amsa tambayar da ke bakunan jama’a ba, cewa: Shin nawa ne dukiya da kadarorin Jonathan? Sai dai ya zuwa yanzu, kafar da ta aro labarin daga tushensa, ta birkita bayaninta, inda ta share sunan Shugaba Jonathan daga jerin wadanda aka ambata.
Kafar da ta watsa labarin, ta kare kanta da cewa labarin nan ya dogara ne da bincike kuma ta dauko shi ne daga wata kafa wacce ta gudanar da faffadan bincike kan batun. Duk da cewa wannan kafa da ta aro labarin ta share shi daga taskarta, amma ainihin kafar da ta buga shi da farko mai suna Celebrity Net Worth ba ta share shi ba, yana nan a yanarta. A zahiri, inda al’amura suke gudana lami-lafiya, babu wanda zai maida hankali kan irin wannan labari daga wata kafa da take lungu, bare ma har a damu da shi. Sai dai wani abin la’akari a nan shi ne, Jonathan ya ki ya bayyana kadarorinsa da dukiyarsa a sarari, wanda haka ya sanya ake ta sukarsa. An ma ji Shugaban yana cewa: “Batun bayyana dukiya da kadarori a bainar jama’a, al’amari ne na ra’ayin kashin kai, dalili ke nan ma ya sa ban damu da yin haka ba, duk yadda kuka kai ga suka da kyara ta.” Babu shakka, irin wadannan batutuwa da yake furtawa a kan al’amura masu tsauri haka a kullum, sun ishi mutane kuma su ne ke kara jawo bakin jini.
A 2007, bayan rantsuwar kama aiki, marigayi Shugaba Umaru Musa ’Yar-aduwa ya bayyana dukiya da kadarorin da ya mallaka a bainar jama’a. A wannan lokacin Jonathan, a matsayinsa na Mataimakin Shugaban kasa, ya bayyana dukiyarsa a N295,304,420.
Duk da cewa babu dokar da ta ce lallai ne sai Shugaban kasa ko Mataimakinsa sun bayyana kadarorinsu karara ga al’umma, kuma duk da cewa Cibiyar Kula Da da’ar Ma’aikata (Code of Conduct Bureau) ta ce Jonathan ya riga ya bayyana kadarorinsa kamar yadda doka ta tanada, amma dai ya kamata a ce cibiyar tana bayyana wa duk wanda ya nemi bayani irin wadannan bayanai, ba wai ta rika boyewa ba.
A ganinmu, hanyar da kawai za a bi a magance jita-jita da shaci-fadi, shi ne ta hanyar fayyace al’amura ga al’umma dalla-dalla daga hukuma ko jami’anta. Rashin bayyana kadarori da masu rike da madafun iko suke yi a Najeriya, musamman ma Shugaba Jonathan, shi ne daya daga manyan dalililan da suka sanya aka hana Najeriya kujera a kungiyar kawancen kasashe Masu Gaskiya, wadda kungiya ce da ke yaki da almundahana a duniya baki daya, wacce kuma aka kafa a 2011 da nufin bunkasa mulkin gaskiya da adalci a duniya. Hukumar Kula da da’ar Ma’ikata ba ta da wani dalili da za ta hana mutum irin wannan bayani na kadarorin shugabanni idan ya nema, tun da yin haka kamar yin biyayya ne ga dokar ’Yancin Samun Bayanai.
Gwamnatin Jonathan ta dade tana nuna ko-in-kula da batun yaki da almundahana, cin hanci da rashawa, musamman ma ta yadda ta rage wa hukumar EFCC karsashi. Don haka irin wadannan bayanai da ake yadawa game da Shugaban kasa, ba shigar da kara a kotu ne zai magance su ba. Babban abin da zai magance haka shi ne, hukumomi da jami’ai su rika bayyana al’amura karara ga jama’a kai tsaye. Hakan zai rage ko kuma ya dakile jita-jita da shaci-fadi da zarge-zargen cewa Shugaban kasa da na kusa da shi sun mallaki kazamar dukiya.