Malaman Islama a Jihar Kano sun tilasta gwamnatin jihar sauya sunan titin ‘France Road’ da ke birnin Kano zuwa ‘Madina Road’ saboada kalaman batanci da Shugaban Kasar Faransa Emmanuel Macron ya yi ga Manzon Allah da addinin Musulunci.
Kungiyar alaramommi da wasu kungiyoyi masu zaman kansu sun kuma bukaci Gwamnatin Jihar Kano ta yanke mu’amala da duk wani abu da ya shafi kasar Faransa.
- Sheikh Sudais ya yi tir da masu batanci ga Annabi
- Batanci ga Annabi: Ya kone motarsa saboda kin Faransa
- Batanci ga Annabi: Shugaban Turkiyya ya nemi a daina sayen kayan Faransa
- Zanen batanci ya kara tsamin dangantaka tsakanin Iran da Faransa
Sakataren kungiyar alaramommin, Dakta Saidu Ahmad Dukawa, bayan taronsu a Masallacin Al-furqan a ranar Lahadi ya kuma kirayi gwamnatin Kano ta cire harshen Faransanci daga jerin harsunan da za ake koyarwa a makarantun jihar.
Alaramommin sun kuma cimma matsaya cewa Musulmi su ci gaba da nuna kiyayya ga Macron da duk wani abu da ya shafi kasarsa ta Faransa.
Sun kara da kira ga Musulmi su ci gaba da addu’o’in la’anta da tabewa ga Macron da daukacin masu goya masa baya.
Malaman sun kuma ankarar da Musulmin duniya cewa hakki ne da ya rayata a kansu kare kima da darajar Fiyayyen Halitta Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam.
Daga karshe kungiyar ta jinjina wa shugabanin da suka fito suka la’anci kalaman batancin da Macron ya yi.