✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Batanci ga Annabi: Muna goyon bayan hukuncin kisa

Malamai da kungiyoyi a Jihar Kano sun caccaki masu sukar hukuncin Babbar Kotun Musulunci

Gamayyar malaman Musulunci da kungiyoyi masu zaman kansu a Jihar Kano sun bayyana goyon baya dari bisa dari ga hukuncin kisa ta hanyar rataya da kotu ta yanke wa wani matashi da ya yi batanci ga Manzon Allah (SAW) a Jihar.

Sun yaba da yadda aka yi saurin yi wa tufkar hanci ta hanyar tsare matashin da yanke masa hukunc, sannan suka caccaki ‘kungiyoyin da masu tutiyar kare hakki’, da ke kushe hukuncin ba tare da lura da dokokin jihar da aka aikata laifin ba.

Sanarwar ta Shugaban kungiyar, Farfesa Musa Muhammad Borodo, ta ce, “Muna kara kira ga masu da’awara kare hakki da cewa a koyaushe su rika fifita amfanin al’umma fiye da na son zuciya.

“Abin da ya fi dacewa shi ne su mayar da hankali wajen yayata kare mutunci da hadin kan al’umma ba surutai ba na neman yayata baudaddun manufofin iyayen gidansu na kasashen waje ba”.

Malaman da kungiyoyin sun jinjina wa Gwamna Abdullahi Ganduje kan yadda ya bayyana shirinsa na mutunta doka da kuma fifita abun da al’ummar da yake jagoranta suka dauka da muhimmanci.

Idan ba a manta ba wata Babbar Kotun Musulunci a Jihar Kano ta yanke wa wani matashi mai suna Aminu Yahaya Sharif hukuncin kisa ta hanyar rataya, bayan kama shi da laifin yin batanci ga Manzon Allah, Annabi Muhammad (SAW).