Ranar Litinin ita ce ranar da aka sanya domin fara sauraren daukaka karar hukuncin da wata kotun shari’ar Muslunci a Kano ta yanke wa wasu matasa da suka yi batanci ga Annabi (SAW).
Kotun dai an gabatar mata da daukaka karar Yahaya Aminu Shariff mai shekaru 22 wanda aka yanke wa hukuncin kisa ta hanyar rataya, sai kuma Umar Faruk mai shekaru 13 da aka yanke wa hukuncin daurin shekara 10.
- Batanci ga Annabi: An yanke wa mawaki hukuncin rataya
- Batanci ga Annabi: Falana zai daukaka karar hukuncin kisa
- Batanci ga Annabi: Falana ya yi karar Gwamnatin Najeriya
- Zan gaggauta sa hannu a rataye mai batanci ga Annabi —Ganduje
Sai dai lauyoyinsu ba su samu halartar zaman kotun ba saboda rikicin #EndSARS a Jihar Legas, inda daga nan lauyoyin za su taso zuwa Kano domin kare masu daukaka karar.
Lauyoyin sun aike wa wani mai suna Zubairu Suleiman Usman sakon waya wanda ya gabatar da korafin nasu ga kotu.
Sun bukaci a dage zaman kotun zuwa ranar 26 zuwa 30 ga watan Nuwamba.
Sakamakon haka, alkalin kotun, Mai Shari’a Nasiru Saminu ya dage zaman zuwa ranar 26 ga watan Nuwamba mai kamawa 2020.