✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bata-gari sun yi yunkurin kone caji ofis a Legas

Jami'an ’yan sanda sun yi nasarar tarwatsa fusatattun matasan.

’Yan daba dauke da makamai sun yi yunkurin kone ofishin ’yan sanda na Oke-Odo a Karamar Hukumar Alimosho ta Jihar Legas kan zargin wani jami’in dan sanda da kashe wani farar hula.

Rahotanni sun nuna yadda jami’in dan sanda ya harbe mutumin yayin da suke sintiri a yankin Ile-Epo a ranar Lahadi.

A safiyar Litinin matasan yankin suka fara shiga zanga-zanga kan kashe mutumin, wanda ba ya dauke da makami, da jami’in dan sandan ya yi.

Zanga-zangar da aka fara cikin lumana ta koma tashin hankali bayan da wasu bata-gari suka shiga farmakar wadanda ba su ji, ba su gani ba.

Wani mutum mai suna Baba Taofeek, ya ce zanga-zangar da Kungiyar Ma’aikatan Sufuri ta Kasa (NURTW), ta faro ta koma tashin-tashina, yayin da bata-gari suka farmaki ’yan sanda.

“Ba don ’yan sanda sun zo a kan lokaci ba, da tuni bata-garin sun kone caji ofis din Oke-Odo. Amma jami’an ’yan sanda sun tarwatsa fusatattun matasan,” inji shi.

Yayin da aka tuntubi kakakin ’yan sandan Jihar Legas, Muyiwa Adejobi, ya bayyana cewa yana hada rahoto kan lamarin, kuma zai sanar da manema labarai yadda ake ciki da zarar ya kammala.