✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bata-gari sun kashe jami’in kwastam a Jigawa

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa ta ce miyagu sun harbe jami’in Kwastam tare da raunata wani a Karamar Hukumar Ringim ta jihar a yayin da…

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Jigawa ta ce miyagu sun harbe jami’in Kwastam tare da raunata wani a Karamar Hukumar Ringim ta jihar a yayin da suke sintiri.

Kakakin Rundunar, SP Abdu Jinjiri, ya tabbatarwa da manema labarai faruwar lamarin a ranar Litinin.

“A ranar 25 ga watan Oktoba 2020 mun samu rahoton wasu bata-gari sun harbe wani jami’in Kwastam tare da raunata abokin aikinsa, yayin da suke sintiri a kauyen Kyarama.

“Sannan ana zargin cewa bata-garin sun yi awon gaba da makaman jami’an kwastam din”, inji Jinjiri.

Ya sanar da cewa rundunar ’yan sanda a jihar na ci gaba da fadada bincike domin gano wadasnda suka aikata laifin.