✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bata-gari sun yashe rumbunan kamfanoni a Abuja

Daruruwan matasa a ranar Lahadin sun shiga rukunin masana’antu da ke yankin Idu, Abuja, tare da yashe rumbunan kamfanonin. Shaidu sun ga yadda bata-garin suka…

Daruruwan matasa a ranar Lahadin sun shiga rukunin masana’antu da ke yankin Idu, Abuja, tare da yashe rumbunan kamfanonin.

Shaidu sun ga yadda bata-garin suka rika yin awon gaba da buhunan shinkafa, sukari, kwalayen madara da sauran kayayyakin abinci.

Duk da bayyanar ’yan sanda bata-garin sun ci gaba da kwasar kayan.

Wasu daga cikinsu sun zo je wurin da babura masu kafa uku, wasu kuma da babur domin kwasar kayan a kai.

Sai dai daga bisani ’yan sanda sun harba hayaki mai sanya hawaye don tarwatsa dandazon mutanen.