✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bassirou Diomaye Faye: Wane ne ɗan adawar da ya zama Shugaban Ƙasar Senegal?

Zaɓe na da aka yi ya nuna al’ummar Senegal sun amince su tsame kansu daga abubuwan da suka faru a baya.

A ƙarshen makon da ya gabata ne aka zaɓi dan jam’iyyar adawa, Bassirou Diomaye Faye a matsayin Shugaban Kasar Senegal, duk da cewa kawo yanzu ba a tabbatar da hakan a hukumance ba.

Amma dai a ranar Juma’a ne ake sa ran Kotun Daukaka Kara da ke Dakar, babban birnin ƙasar za ta sanar da sakamakon ƙarshe a hukumance.

Al’ummar Senegal miliyan bakwai da dubu 300 suka ziyarci rumfunan zabe domin zabar shugaban kasar na biyar, bayan Leopold Sedar Senghor da ya mulki ƙasar tsakanin 1960 zuwa 1980, sai Abdou Diouf daga 1981 zuwa 2000, Abdoulaye Wade daga 2000 zuwa 2012 da Macky Sall da ya karɓi kasar daga 2012 zuwa 2024.

Wane Bassirou Diomaye Faye?

Bassiorou Diomaye Faye, mai shekara 44, ya zama Shugaban Senegal mafi ƙarancin shekaru a tarihin ƙasar.

An haifi Diomaye Faye a ranar 25 ga Maris na 1980, a ƙauyen Ndiaganiao da ke yankin Thies na ƙasar Senegal.

Ya yi karatun digiri na biyu a fannin shari’a, kuma ya gama digirin farko a Makarantar Ƙasa ta Nazarin Gudanarwa da Mulki.

A 2007 ya fara aiki da Hukumar Tattara Haraji ta Ƙasa sannan a 2014, ya kafa jam’iyyar Pastef ta ’Yan Kishin Afirka.

An kama shi a ranar 14 ga watan Afrilun 2023 tare da zarginsa da laifin “daƙile ayyukan jami’an tsaro” bayan ya yi watsi da tsarin shari’ar da aka bi wajen hukunta uban gidansa Ousmane Sonko.

A ranar 14 ga wannan wata na Mayu ne aka saki Bassirou Faye da Ousman Sonko daga gidan yari bayan afuwar da shugaban ƙasar ya yi musu.

Sakamakon yadda ba a taɓa tuhumarsa da aikata babban laifi, ko gurfanar da shi a gaban kotu ba, ya samu damar tsayawa takarar shugaban ƙasa.

Diomaye Faye, wanda jama’a ba su san shi sosai ba har zuwa shekara ɗaya da ta gabata, ya samu farin-jininsa ne bayan gallaza wa jam’iyyarsa ta Pastef da aka yi a baya-bayan nan.

Sai dai kuma abin da ya fi ɗaga martabarsa shi ne yadda madugun ’yan adawar Senegal Ousmane Sonko ya ce a zaɓe shi a matsayin shugaban ƙasa.

Masu sanya idanu sun bayyana cewa nasarar Diomaye Faye da jam’iyyarsa wani juyin-juya hali ne na siyasa kuma zai sanya a sauya tunani a harkokin siyasar ƙasar.

Faye na kallon kansa a matsayin ɗan takarar kawo sauyi da kishin Afirka baki ɗaya.

Manufofinsa sun haɗa da dawo da martaba da ƙimar Senegal, wadda ya ce an sayar wa ’yan ƙasar waje ita.

Ya kuma yi alƙawarin yaƙar cin hanci da rashawa, tare da raba arzikin ƙasa a tsakanin jama’a.

Faye ya kuma yi alƙawarin sake duba yarjejeniyoyin haƙar ma’adanai, iskar gas da albarkatun man fetur a ƙasar da ta shirya fara haƙo mai da gas a ƙarshen shekarar nan ta 2024.

A lokacin yaƙin neman zaɓe Faye ya bayyana kansa a matsayin wanda zai kawo sauyi a ƙasar ta yammacin Afirka mai yawan mutane miliyan 18.

Cikin alƙawurran da ya yi har da rage biyayyar da Senegal ɗin ke yi wa uwargijiyarta Faransa da kuma daina amfani da takardar kuɗi ta CFA.

Ƙasashen duniya sun sanya idanu sosai kan zaɓen na Senegal, wanda ya zo bayan tashin-tashinar siyasa ta tsawon shekara uku a ƙasar da take ɗaya daga mafi zaman lafiya a Afirka.

Senegal ƙasa ce da ta ƙulla alaƙa mai ƙarfi da Yammacin duniya a lokacin da Rasha ke ƙoƙarin ƙara saita kanta a yankin ta hanyar ƙulla ƙawance da ƙasashen Sahel.

Macky Sall ya taya Bassirou murna

Shugaban ƙasar Senegal Macky Sall ya taya Bassirou Diomaye Faye murnar lashe zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar ranar Lahadi, 24 ga watan Maris.

“Ina yabawa game da yadda aka yi zaɓen shugaban ƙasa na ranar 24 ga watan Maris, 2024 ba tare da matsala ba.

“Ina kuma taya murna ga wanda ya yi nasara, Mista Bassirou Diomaye Faye, wanda alamu suka nuna cewa shi zai yi nasara. Wannan nasara ce da dimokuraɗiyyar Senegal,” in ji Sall a sakon da ya wallafa a shafinsa na X ranar Litinin.

Sall ya fitar da saƙon ne jim kaɗan bayan tsohon Firaministan Senegal kuma ɗan takarar gamayyar jam’iyyu masu mulki ya karɓi shan kaye a hannun ɗan takarar jam’iyyar adawa a zaɓen shugaban ƙasa.

Amadou Ba, ɗan takarar jam’iyya mai mulki ya faɗa a wata sanarwa daga ofishin kamfe ɗinsa ranar Litinin, cewa yana taya murna ga ɗan takarar jam’iyyar adawa, Bassirou Diomaye Diakhar Faye, kuma yana yi masa fatan alheri.

Sakamakon farko ya nuna cewa Faye ya samu aƙalla kashi 57 na ƙuri’un da aka kaɗa, yayin da Ba ya samu kashi 31.

Nasarar da ya samu a zagayen farko na zaɓen ta dace da abin da aka gani na yadda mutanen ƙasar ke nuna ɓacin-ransu da rashin aikin-yi da shugabanci nagari a ƙasar da ke Yammacin Afirka.

Jawabin Bassirou Diomaye Faye bayan lashe zaɓe

Zaɓaɓɓen shugaban Senegal Bassiorou Diomaye ya yi alƙawarin yin mulki tare da ƙan-ƙan da kai da kuma nuna gaskiya.

Ya bayyana haka ne a jawabinsa na farko bayan zaɓen shugaban ƙasar da aka yi ranar Lahadi.

“Zaɓe na da aka yi ya nuna al’ummar Senegal sun amince su tsame kansu daga abubuwan da suka faru a baya,” kamar yadda ya faɗa wa ’yan jarida a ranar Litinin.

“Na yi alƙawarin yin shugabanci tare da ƙan-ƙan da kai da kuma gaskiya.”

Ɗaya daga cikin manyan ƙudurorinsa a matsayin shugaban ƙasa shi ne “haɗa kan ’yan kasa” sakamakon yadda aka shafe shekara uku ana tashin hankali da kuma rikicin siyasa a ƙasar, kamar yadda Mista Faye ya bayyana.

Ya kuma yi alƙawarin “yaƙar cin hanci a kowane mataki” da sake gina hukumomi tare da magance matsalar tsadar rayuwa.

Mista Faye ya kuma gode wa shugaba Macky Sall mai barin gado ganin yadda ya taimaka aka gudanar da zaɓe cikin cikin nasara.