✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Bashir Dandago ya bayyana a kotu

Ana zargin mawakin yabon da neman tayar da fitina da kuma zagin malamai

An kai fitaccen mawakin yabon Manzon Allah (SAW) Bashir Dandago gaban kotu, bisa zargin neman tayar da zaune tsaye a Jihar Kano.

A halin yanzu an riga an kai mawakin Kotun Majistare da ke unguwar  Nomansland, ana  jiran isowar lauyan gwamnati don fara shari’ar zargin Bashir Dandago da neman tayar da tayar da tsaye.

Hukumar Tace Fina-finai da dabi’i ta Jihar Kano ce ta tsare mawakin bisa zargin sa da neman tayar da fitina a Jihar a wata sabuwar wakar da ya fitar wadda a cikinta yake zagin wasu fitattun malaman Islama.

Sugaban Hukumar, Isma’ila Na’abba Afakalla ya ce a cikin wakar da mawakin ya fitar ba bisa ka’ida ba, ya rika goyon bayan Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara, wanda ake zargi da cin zarafin Sahabban Manzon Allah (SAW).