Bashin da ake bin Najeriya na ci gaba da taruwa inda zuwa watan Yunin 2020 yawansa ya kai kimanin Naira tiriliyan 31, sabanin Naira tiriliyan 28 din da ake bi a watan Maris.
Ofishin Kula da Basussuka na Kasa (DMO) shi ne ya tabbatar da alkaluman a rahotonsa na wucin gadi da ya fitar ranar Laraba.
A cewar rahoton, basussukan sun hada da na Gwamnatin Tarayya, jihohi 36 da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja.
Kudaden sun karu ne cikin watanni uku sakamakon bashin Dala biliyan 3.36 da aka kara ciyowa daga Asusun ba da Lamuni na Duniya (IMF) domin cike gibin kasafin kudin 2020 da aka yi wa kwaskwarima, da kuma samar da Naira biliyan 162.557 na shirin Sukuk sai kuma kudaden da za a biya bashin da masu fiton kaya ke bi.
Kazalika ofishin na DMO na hasashen kudaden za su iya karuwa yayin da za a kara ciyo wani a cikin gida da kuma wanda za a kara karbowa daga Bankin Duniya, Bankin Raya Kasashen Afirka (AfDB) da kuma Bankin Raya Musulunci domin aiwatar da kasafin 2020.
Idan dai za a iya tunawa sai da Najeriya ta yi wa kasafin 2020 kwaskwarima ta hanyar rage shi saboda illar da annobar COVID-19 ta yi wa tattalin arziki da ma kudaden shigar da gwamnati ke samu a bana.