✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Bashin $5.3bn ya hana gina layin dogo daga Kano-Ibadan

Da zarar Najeriya ta samu bashin daga China za a fara aikin titin jirgin kasan

Gwamnatin Tarayya ta ce da zarar ta samu bashin $5.3bn daga kasar China, za ta shiga aikin gina titin jirgin kasa daga Ibadan zuwa Kano.

Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi ne, ya bayyana hakan a Abuja ranar Asabar.

Amaechi ya ce “har yanzu ba mu samu rancen bashin da muka nema daga kasar China na $5.3bn ba, da zarar mun samu za a fara aikin.

“Lokacin da na sanar da cewar, an kulla yarjejeniya da kamfanin gine-gine na CCECC na kasar China, mutane sun dauka cewa a lokacin za a fara aiki.

“Ba haka abun yake ba, ba mu aike musu neman bashin kudin ba sai bayan shekara daya da kulla yarjejeniyar,” inji Amaechi.

Ministan ya kara da cewar aikin titin jirgin kasan daga Ibadan zuwa Kano, zai hade garuruwa shida da zarar an kammala shi.

Wadannan garuruwa su ne; Kaduna, Kano, Abuja, Minna, Ilorin, Osogbo da kuma Ibadan.

Sannan ya ce ana kammala aikin, jirgin kasa zai rika dauko kaya daga Legas zuwa Kano kai tsaye.