Basaraken kabilar Tangale a jihar Gombe, Dakta Abdu Buba Maisharu II ya rasu.
Ya rasu da yammacin ranar Lahadi yana da shekaru 72 a duniya, kamar yadda Gwamnatin Jihar Gombe ta tabbatar a wata sanarwa.
- Kano Pillars na neman dan wasanta ruwa a jallo
- COVID-19: Tsohon gwamnan jihohin Kano da Binuwai ya rasu
Sanarwar, wacce Sakataren Gwamnatin Jihar, Farfesa Ibrahim Abubakar Njodi ya fitar, ta ce basaraken ya rasu ne bayan wata gajeruwar jinya a Asibitin Koyarwa na Gwamnatin Tarayya dake Gombe.
“Muna bakin cikin sanar da rasuwar Mai Tangale na 15, Dakta Abdu Buba Maisheru II, wanda ya rasu ranar Lahadi, 10 ga watan Janairun 2021, bayan gajeriyar jinya yana da shekaru 72,” inji sanarwar.
Daga nan sai gwamnatin ta bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga masarautar, jihar Gombe da ma kasa baki daya.
Sanarwar ta kuma yi addu’ar samun rahama ga mamacin da kuma fatan jure rashinsa ga iyalai da masarautarsa.
Kazalika, gwamnatin ta ce nan ba da jimawa ba za a sanar da yadda biki binne shi zai gudana.
Dakta Abdu Buba dai basarake ne mai daraja ta daya kuma fadarsa na garin Billiri a jihar Gombe.
A watan Mayun 2020 ya kamu da COVID-19, amma daga bisani ya warke.