An gurfanar da wani basaraken kabilar Igbo wanda ya lashi takobin gayyatar kungiyar ta’addanci ta IPOB zuwa a Jihar Legas.
A yayin da yake barazanar gayyatar IPOB domin kare duniyoyin ’yan kabilar Igbo a Legas, Nwagu ya ce kungiyar za ta koya wa mutanen jihar hankali.
- An bude kasuwar da aka rufe saboda kazanta a Abuja
- Yadda likita ya yi wa mara lafiya fyade a asibiti
Bayan barazanar Frederick Nwagu ga rayuka a dukiyoyin jama’ar jihar ta hanyar amfani da IPOB ne a ranar 1 ga watan Afrilu jami’an hukumar tsaro ta DSS da ’yan sanda suka cafke shi.
Gwamnatin Jihar Legas ta gurfanar da shi a gaban babbar kotun jihar bisa zargin, “yunkurin ta’addanci da halartar taro da nufin daukar nauyin ’yan ta’adda.”
Sai dai Nwagu, wanda shi ne tsohon shugaban ’yan kabilar Igbo da ke rukunin gidaje na Ajao da ke jihar, ya musanta zargin.
Alkalin kotun, Mai Shari’a Y. A Adesanya ya dage sauraron karar zuwa ranar 4 da kuma 5 ga watan Yuni, 2023.