Wasu da ake zargi masu garkuwa da mutane ne sun kai hari a fadar wani basarake kimanin sati biyu da ba shi sarauta a Jihar Legas.
A ranar Lahadi maharan suka kai hari a Fadar Isiu da ke yankin Ikorodu inda suka yi ta harbi kan mai uwa da wabi a harabar.
“An harbi sama da mutum 60 kuma an kai wadanda suka samu raunuka asibiti ana kula da su”, inji Oba Okukayode Raji wanda a ranar 24 ga watan Agusta Gwamnatin Jihar ta ba shi sandar sarauta.
Basaraken ya ce maharan sun mamaye gidansa a ranar Lahadi kafin daga bisani ‘yan bangar yankin su kawo dauki su kora su.
“Ba mu ankara ba sai muka fara ganin bakin fuskoki da wasu samari sun tunkaro fadar dauke da makamai iri-iri.
“Da suka matso kusa sai suka fara harbe-harbe; ta hakan ne aka raunata daya daga cikin ‘ya’yana”, inji basaraken.
Ya ce ya tuntubi Babban Baturen ‘Yan Sandan yankin domin kawo msusu dauki, sai dai, “Sun zo a makamare, amma suka baza mutanensu su yi sintiri a cikin yankin.
“Mutum uku daga cikin wadanada ake zargi da hannu a harin sun shiga hannu”, inji shi.